Hausa novels

ASALINA Hausa novels document by Maryam Ismail

ADVERTISEMENT
 
Book Contact INFORMATION
Book ASALINA
Author Maryam Ismail
Uploader Mansur Usman Sufi
Image Credit Sufi Graphic
Size 136kb
File txt
Date 9 APRIL 2023
Group kainuwa writers Association
Tages Romantic 
PROLOGUE
 
Da sauri sukayi kanta Manab ya dauko glass cup da ruwan sanyi yana zuba mata yana fadan “Amma na ki tashi don Allah”.
 
A hankali ta soma bude ido tana binsu da kallo,sosai ta rike Abee tana kuka lokacin da ta tuna abunda ke faruwa.
 
” yanzu kana nufin Minad ta tafi ta barmu?,wanne irin bakin ciki ne wannan me ta aekatawa wani”.
 
“Kiyi hakuri kaddara ce ta kama haka idan Minad rabanmu ce zata dawo garemu,kuma kinga yan sanda na bincike akan lamarin” Alhaji Aminu ya fada.
 
Nan dai sukaita ta bata baki harta hakura ta rungumi kaddarar data iso garesu.
 
Wasawasa abun yaci tura duk inda ake tunanin Minad ba’a sameta ba har sun hakura sun fallafawa Allah al-amarinsa suna addu’ar samun zabin alkairi dukda damuwa na damunsu.
Rike da plate din abinci Momy ta fito kai tsaye dakin Jawad ta nufa ,can jikin bango kusa da bed ta gansa ya hada kai da gwaiwa,a hankali ta dafasa tace”Mike damunka Jawad ka duba yadda ka koma,baka cin abinci kullun sai damuwa”.
 
Hawayen idonsa ya goge yace”Momy yanzu mun rasa Minad kenan?,gaskiya Wanda ya dauketa bashi da imani,kuma na ganesa sai munyi shara’a don bazan taba yafe masa ba”.
 
“A’a Jawad ka daina fadan haka,Ku mata addu’a zaifi “
 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button