Uncategorized

Hassada ita ce mafi girman abar da na gani ido da ido a duniyar Marubuta. Mujahida Matar Malam

ADVERTISEMENT

 

Hassada ita ce mafi girman abin da na gani ido da ido a duniyar Marubuta

Cewar Marubuciya

Mujahida Matar Malam

Assalamu alaikum Barka da zuwa shafin LITTAFANYAKI.COM.NG


da ke kawo maku fira da marubutan Hausa da ma littattafan su . 

Wanda ni MANSUR USMAN SUFI zan jagoranta
A wannan makon a karon farko zamu fara tattaunawa da fasihiyar marubuciya mai alƙalamin zinare, kar dai na cika ku da bayani da farko muna yi wa baƙuwarmu barka da zuwa, masu karatu za su so mu ji takaitaccen tarihin baƙuwarmu ?….

“`Assalamu'Alaikum
Yawwa brk Dai Ina Gdy, 🙏 naji dad'in had'uwa daku inamuku fatan Alkhairy musamman gareka MANSUR USMAN SUFI ...

  Tarihina dai shine...

Sunana ✍️ Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝, Kuma Ni haifaffiyar Y'ar garin Sokoto ce, najima Ina Sha'awar Rubutu Ina karantawa sosai, musamman littafan yak'i Gsky nafi sonsu Domin ada Sune Kawai Nafi karantawa tin Ina Yarinya Sosai, daga Baya sai naji Ina Ra'ayin Nima nafara Rubuta labari dakaina, saikawai Nafara amma saina Sauya Akalar K'wak'walwata daga na yak'i, zuwana soyayya dama Fad'akarwa domin cikinsune Kawai Zan iyabada sak'onda nakeson isarwa cikin sauk'i, Kamar wa'azantar ilimantarwa Fad'akarwa wayarda Kai, Ahankali Kuma saina Fara na HORRO Saidai bancika yinsuba gsky Domin basa bada Irin sak'on da nakeson badawa na wa'azantar ilimantarwa Fad'akarwa wayarda Kai, iyakarsu Nishad'i kawai...“`

Masha Allah a wace shekara kika fara rubutu kuma mene ne ya ja hankalinki?

“`Gaskiya Anjima Sosai da fara Rubutuna Dan tinkan nayi waya lokacin marubutan online basu sosai Kuma Kuma dai Banda Android keypad ce, kawai nakanyi ko a Littafi ko wani gun daban amma 2019 nafara Rubutun online...

Abunda yafi Jan hanakalina Nima Inason nashiga dagacikin masu Wayardakan AL'UMMA cikin sauk'i, Kuma tahankane kawai Zan iya Fad'ar aibun wata halayyar tareda hanyar gyarata batareda Wanda na fad'awa yahasala ba, bawai Dan neman suna yasa nashiga Rubutuba a'a dan nafad'akar ilimantarwa wa'azantarwa Kuma Alhmdllh sak'ona yana zuwa inda nake burin zuwanshi..“`

Mene ne bambancin da ke tsakanin littattafan yaki da na soyayya?..

“`banbancin Anawa ganin domin Ina karantawa Kuma inad'an gwada Rubutawa, kunsan abaya nafad'amuku Nafison irinsuma, to Anawaganin banbancin Nishad'i

Banbancin dai Kamar K'agagangen labari ne dana Gsky,

MISALI

littafin yak'i jarumanda Za'asaka fad'anda suke da jarumtarsu duk labarine kawai damai Fassarar rubutasu zaiyi Amfanidasu, domin Abun idan jarumin littafin yayi kasan littafine kawai Bawai akwai a zahiri bane, Koda Akwai to Akwai Wani banbanci, kaga kenan koyaya ne dole NISHAD'ANTARWA tashiga cikin Labarin...

LITTAFIN Soyayya kuwa

MISALI

Wa'azantar zaka iyazama kadube rayuwar Abokinka yana wani mugun hali Kuma bazaka iyafad'amasa abun kuskure bane saboda kanajin nauyinsa saikawai ka Rubuta Labari Akwai tareda Nuna illar wannnan rayuwar dayake bashi kad'ai zaiganiba wani zaigani so idan yanada rabo saikaga yagyara kaga Kenan marubucin Yabada sak'on wa'azantar ilimantarwa Cikin sauk'i...

Amma Duka marubuta na yak'i Dana Soyayya Gsky suna k'ok'ari kuma sunada baiwa Kuma suna bada taimakon gyara ga AL'UMMA so Dukansu Ina Alfahari dasu Kuma inajinjina musu dama fatan Alkhairy“`

Wane ƙalubale kika taɓa fuskanta a rubutu da ba za ki manta da shi ba ?

“`Hassada itace Babban K'alubalina Dana gani Ido da Ido Aduniyar marubuta, Naga Hassada munafurci K'iyayya da tsana, har sukasa najefarda Alk'alamina najuya daniyar daina Rubutu Gaba d'aya, amma Cikin Ikon Allah dama k'ok'arin Masoyana Zuma makaranta littafaina wllh sukadage Saida nadawo duniyar marubuta, so Gsky K'alubalaina sune Hassada munafurci K'iyayya da tsana>>>> Kuma bazan mantaba harzuwa mutuwa Domin inda banyi zatoba Hassadar da munafunci zuwa tsana Suka Fara fita shiyasa bazan mantaba Amma inacikin yafiya wad'anda suka cutan nayafe musu fatana Allah yamun afuwa nima, kuma Ina musu fatan Shiriya idan sunada rabo, idan babu Allah kaimuna tsari dasu....“`

Wane abu ne ke ci miki tiwo a ƙwarya game da sha’anin marubuta?

“`Rubutun Batsa, shine Abunda yake damuna Sosai wallahi, yakecimin tuwo a k'warya, Amaimakon Kullum Asami sauyi Saidai kaga Abun yana dad'a ta'azzara, sunata lalatamuna tarbiyar yara maza dama Mata, wasu silarsuma suke Aikata Alfasha, Kuma Abunda nakeson su wad'annan marubutan sugane shine Ainahin marubutanmu na farko Wllh ba haka sukeba Sam ba Batsa Cikin labaransu, Amma su nasu bama zaka Samu wani Abu nad'aukar darasiba duk miyagun Abubuwane kawai ciki, idan kayi magana saikaji sunce Wai Gyaran Aure suke yo Ina Gyaran Aure ga b'ata tarbiya, niganina basai kafito kafad'e komai bayyane ba Kawai kasakaya kowama zai fahimta ai, amma ina wata inkaga littafinta saima kaji kunyar Akiraka marubuci wllhi, gashi basuson Shawara kanayin niyar fad'amawata saikaji tafara masifa kokaji Ance kada Y'ar under 18 takaranta min Littafi, kaidajin hkn kasan babu Albarka kuma babu abin arziki nanma zaka gane Bawai gyara tashiryayiba sai b'atawa idan Gyaran tsakani da Allah ne Meyasa Za'a cire 18 year's.... Kuma makaranta kuyi nazari da wannnan Abun Kuma kuyiwa kanku fad'a sannan kuji tsoron Allah, Domin mutuwa Bata sallama ko neman izini zuwa Kawai take ta d'auke mutum, sannan duk Abunda kamutu Akai Za'a tasheka Akai saboda Haka Ina bada Shawara Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nida Duka marubuta dama makaranta WLLAHI muji tsoron Allah“`

Mene ne babban burinki a rubutu?

“`burina Bai ta Allakanan kawaiba Inason K'arin Ilimi sosai domin K'ara Fad'akarwa, Wa'azantar duka....

Rubutun Kuma Inason nafara buga littafi nak'ara shahara ta kowanne fanne mutane Susanni kuma Susan manufata dama sak'onda nakeson isar musu, Rubutuna yazaga ko Ina Aduniya, Kuma inafatan tasilar Rubutuna mutane su shiryu su Gyara halinsu makomarsu zuwa gobensu, Kuma Allah yazama silar nawa tsiran gobe k'iyama“`

Akwai abu dake faruwa na za ki samu Marubuta mata a halin yanzu sun koma rubutun gasa,
Basu mayar da hankali akan rubutun su

Shin kwadayin daukaka ne ko kudi.
Da yawa wasu na zargin duk wacce ta ci gasar BBC ko makamantan su da girman kai saboda sun zama wasu
Me za ki ce akan hakan ?

“`Gaskiya ne yanzu kwad'ayin Abun duniya akasawa gaba bawai Dan kayi Rubutu Dan wasu su Amfana bane a'a Saidai Dan suyi shura suzama wani Abu kuma suna Zama Za'a Fara d'agawa Girman Kai walak'anci,

Kawai zance Kwad'ayin Abun duniyane shine yaketafe da son zama wani son Kud'i keta dokar Allah da Sauransu, kawai Kwad'ayin Abun duniya zamu kirashi,

Abunda bamu fahimtaba Shine shifa rabonka baya wuceka duk Abunda Allah yanufa kasamu tofa saika Samu basaika saka kwad'ayi ba,  Koda yaushe muyi hak'uri da rayuwa muzauna inda Allah keson Garinmu,

Nidai Gsky gwanda nayita rubutun Ina Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa zaifimin son Kud'in da d'aukaka Gsky, eh kowa yanason Cigaba Amma zaifi Kyau tazo tahanyar halak so idan muka cigaba dayi saboda Allah zaibamu sakamako muna Zaune ma, nidai wllhi bantab'a Sha'awar Shiga gasar marubuta ba bantab'a yiba Kuma banajin zanyi Dan wllahi Sam baya burgeni ko kad'an

Maganar girman Kai da walak'anci kuwa, Akwai shi ga Marubuta Tabbas nikaina MARUBUCIYAR ce Amma bazai Hana nafad'e Gsky ba, wasu daga cikinmu ba dukaba Gsky sunada girmankai da walak'anci, Kuma Akwai k'eta wllahi, Dan idan MARUBUCI ya iya Abu baka iyaba kadama karok'e yakoyama Dan wllahi bazai koyamaka ba Komai kusancinku kuwa wanima direct zaifito yace kabarshi Kud'i Sannan yakoyama inko bakadasu Saidai ka hak'ura Dan WLLAHI Bai koyama NIKAINA Anshayimin hakan, shiyasa kungani Nan Natsane narok'e mutum Alfarma Natsane narok'e mutum Yarda Ake wani Abu domin Akwai Ciwo ka kada Girmanka karok'e Abu Amma Yak'i koyama, shiyasa duk wani Abu daya shafe Rubutu Ni wllahi ba Wanda yakoyamin Banda Ubangida ba Wanda yakoyamin Komai kawai nakanyi Aiki tuk'uru nayita bitar Abuna dakaina harnaga nayi nasara na iya Batareda taimakon kowaba,  kuma wllahi Alhmdllh idan na iya Ina koyawa mutane Yanzu bansan Adadin mutane nawa na koyawa Rubutu da Sauran Abubuwaba,.. rayuwarmu bazata tab'a Cigababa idan Muna Hassada da k'yashi, Hassada da k'yashi mana inbandasu Taya ka iya Abu Kuma kakasa koyawa d'an uwanka? Ni wllahi Banga Anfanin Arzikinda zai azurtaka Kai kad'aiba kaci ka kad'ai Batareda kowa ya Amfana ba, wannan ma zaihanamu Cigaba wllahi, so mugyara Allah Yasa mudace 🤲“`

Duba da cewa mafi yawan labaran yanzu sun fi mai da hankali akan soyayya.

Shin me a bangaren ki kin taɓa yin rubutu akan cutakan dake damun yara ƙanana ko mata

“`Hunmmmm ☺️☺️ kasani murmusawa,
Kasan me Makaranta nason littafin soyayya muma Duka Mata muna son soyayya🙈🙈🙈🙈 musamman Wadda ba cin Amana ba K'arya ba yaudara CIKINTA, soyayya nada dad'i rayuwar Masoya masu Gsky da Amana Abun burgewace gsky, lokuta da dama cikin littafaina idan inayi Sainaji Inama kowacce macce musamu Adalin miji irin na Mijin novels 📚⁉️⁉️da saki yaudara duk bazasu yawaitaba gsky Inason Soyayya🫶🫶🫶🫶 da Adalin miji Kuma Duka Mata suna so, wannan yasa muke yawan yinsu Kuma Dan k'ara janyo Hankalin mazan suzama Nagari...

Eh Sosai inayima Bawai natab'a yiba, Domin Ni Gsky Cikin littafan nawa takowanne fanne nakan lek'a Gsky Ni burina kawai nabada gudunmuwa wadda zatakawomuna gyara a Rayuwarmu duka,

Littafaina DAYAWA Akwai har wad'anda suka shafe yaudarar maza Kan Mata da sunan Soyayya dama Rashin imani Kuma nabada irin makomarda Allah Yafad'a zai fad'awa Azzalumai,

Littafina na _UCIYAR NAMIJI yana d'auke da darasin cutar da Namiji

AKAN PRE_WEEDING PICTURE Yana bada darasin illar hotunan aure munana damuke

JAMI'IN SIRRI yana nuni da illar zalunci

FATAWAL BUDURWAR MIJINA, yana bada darasin Duka Cutar mutum 2 tsakanin Macce dama Namiji

So Gsky Cikin littafaina inabi ta kowanne b'angaren Komai inatab'awa Gsky Ina Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa ta kowanne b'angarenma``

Zuwa yanzu kin wallafa littatafai kamar nawa kuma mene ne sunayen su wanne ne bakandamiyarki ?...

“` Eh to Gaskiya bantab’a wallafa Littafi ba iya online kawai nake Rubutuna amma inada burin wallafawa very soon in Allah yanufa… Amma daga sannan zuwa yanzu narubuta littafai guda 29 narasa 2 daga Ciki SHIYASA suke guda 29..“`

K'ad'an daga cikinsu Akwai

*MAI ZAMAN KANTA*

*DOCTOR HEESHAM*

*ABBAKAR SARAKIEYY*

*AKAN PRE_WEEDIN PICTURE*

*FATALWAR BUDURWAR MIJINA*

*SANADIN PARTY*

*D'AUKE D'AID'AI DUNIYAR SHAID'ANUUU ☠️*

*SILAR D'A NAMIJI*

*RAUNIN MACCE BAYA HANA D'AUKAR FANSA*

*GUBAR MATSAFA*

*NI DA MISBAH*

*SAURAYINA*

*BAK'IN KISHI*

Da Sauransu

“`Eh to Wanda nafarayi farko FAHAT HOT LOVE, Amma kuma Zan iyacewa mutane sunfi Yawan Anbato neman Abbakar sarakieyy doctor Heesham Mai Zaman Kanta, amma Wanda yafi fiddani Gsky Raunin Macce baya hana d’aukar FANSA>> Alittafaina Kuma ba Wanda banaso ko wannema bakandamiyata ne domin Ana min magana kanshi Gsky Alhmdllh kawai ZANCE“`

Mene ne sakon ki na karshe ga marubuta da makaranta

“`Sak’ona ma K’arshe shine zance suji tsoron Allah su tsalkake Alk’alaminsu, suna mutuwa tana Zuwa Kuma duk Abunda kamutu kana Aikatawa Za’a tasheka Akai so mugyara kabarinmu Kan mushiga, kin Rubuta Batsa kinzo kinmutu waccan takaranta taje Aikata wata wasab’on kisanifa dole Araba zunubin dake Za’a tasheki kiga Abunda Kika Aikata Kunga kenan ke mutu Amma kebar baya da k’ura,. Allah ya tsaremu da Aikin danasani, muda bama Rubutawa Allah yak’ara karemu, suda sukeyi kuma Allah ya shiryesu, inbamasu shiryuwabane Allah kaimuna maganinsu,…. Kuma inabama wasunmu Shawara dasu daina Girman Kai zuwa walak’anci Kuma mucire k’yashi da Hassada Aranmu, Allah ya k’ara karemu yasa mucika da imani muyi K’arshe maikyau Ameen,..  Inayiwa kowa da kowa fatan Alkhairy, kaima maishirin inamaka fatan Alkhairy naji dad’in wannnan Shirin naku. Wassalamu Alaikummm… ✍️ Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝“`

*D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀*

     _PAID BOOK #300 ONLY_

  
     _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

   “`MARUBUCIYAR…  (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d’a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak’in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d’aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA….. And Other’s BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK….(20) SAKACINA PAID BOOK…. (21) SO!!! FREE BOOK… (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR  MIJINA PAID BOOK… (23) D’AUKE D’AI D’AI DUNIYAR SHAID’ANU PAID BOOK
loading….. Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝“`

          _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_   *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY*
      _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

    _26/7/2023 Jully Tuesday_

      *BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*

*Free 🅿️ 1 to 5*

              .......Wani Matashin Saurayi nagani Zaune kusa da Ahlinsa sai fira suke cikin k'aunar juna,

"Samar!" Matar takira sunanshi cikin serious voice, Jin hakan yasa ya maida Hankalinsa kanta Domin ba kasafai take Kiran sunan shi ba, saidai tace tace Soja, hakan ya tabbatar masa Abunda mama zata Fad'i Mai Mahimmanci ne,

"Na'am Umma,"

"Soja kanada Aikinyi Yanzu kuma ko mahaifinka nada Arzikin maka Aure Koda Kai bakada Abun kace Abari kasamu Aiki Yanzu shekara 3 kana Aikin kasami K'arin girma kuma kasami Kud'i to yanzu kasamu Wadda zaka Aura,"

"Mahaifiyar ka nada Gaskiya Yanzu kayi shekara 30 fa to ya kamata kayi Aure soja,"Cewar Abba

Hunmmm: Shikenan In Sha Allah Zan k'ok'arin neman Wadda ta dace,"

"Masha Allah, Allah yakawo tagari,"

Wayarsa tafaru ruri sunan Taj ya bayyana Cikin murmushi yad'aga Kiran Yace "Hello my friend Yane,"?

A d'ayan b'angaren Akace "normal kaga sak'o ta email d'inka Major Yana nemanmu da gaggawa Kan wani Assignment zamuje,"?

Gyara Zaman wayar yayi Yace"Assignment kuma? Bayan Munsami hutun 1 months wane Assignment kuma,"?

"Nima ban sani ba wallahi na d'auka ma kaga sak'on da shine zanyi wannan tanbayar Yanzu mukayi magana dasu Sam itama tayi mamakin Abun Amma koma yayane idan muje Abuja Gobe masani,"

Hunm: "Shikenan badamuwa sai mun had'e goben"

Katse Kiran yayi ya duba Email d'in Tabbas Anason ganinsu gobe,

Fad'ama Iyayensa yayi suka masa fatan Alheri sannan ya hau Shirin tafiya............

**********"""""""""''********

"Sam wai kina macce Amma baki zama ki huta kullum cikin wahala kibar Aikin mana kinga Adangi sai zagina Ake wai nice na d'aure miki gindi kike Aikin maza kina cud'anya dasu,"

"Mommy manta dasu kawai cikinsu ba Wanda ya tab'a taimakon mu bayan rasuwar Baba so Yanzu nayi Aiki tuk'uru nasami Aiki gashi harna Samu K'arin girma to baikamata na watsar da damata ba kawai kimin Addu'a Allah ya kareni"

"Addu'a cikin ta nake kullum sam to Amma maganar Aure fa"?

"Aure lokaci nazuwa Mommy  Amma in Sha Allah namiki Alk'awari muna dawowa Wannan Assignment da Akamuna Kiran gaggawa to zanyi,"

"Shikenan Allah y kareku"

"Ameen mommy na Ina sonki"

"Nima haka yanzu yaushe zaku"?

"Gobe ne, kawaii na shirya kayana ne nasan bazan dawoba daga can zamu wuce Assignment d'in,"

*********""""'''''''''******

"Jidda Yanzu barina zakiyi kije wannan Aikin? Auren mufa saura sati 3 Amma zakije wani Assignment kibar Aikin mana,"

"Kaga Bash Koda kasanni kasanni da Aikina Kuma Ahakan kaji kana iya Aurena so kayi hak'uri Mana kasani ko badogon Assignment bane,"

"Nifa bazan iyaba Ace wai wadda Zan Aura take cud'anya cikin k'attan maza, indai kikaje Assignment d'in to wallahi ki nemi wani mijin," fuuuu yabar wurin,

Baki sake tabishi da kallo wai kada taje to soyake tarasa Aikinta bayan Tasha bak'ar wuya Kafin takai inda take yanzu,"? Tabbd'i wallahi bazatayi dagegeduwa Aiki Kam saitaje,
Shiga gida tayi wani iri hakan Yasa kaka tanbayar ta lafiya kuwa?

  Bata b'oyemata komai ba Dan Batada kowa sai ita iyayenta sunjima da rasuwa take hannun kakar babanta ne,

Tsaki taja Mtssswww "saboda shi kike damuwa manta dashi idan kikaga Auren baiyuba to Allah Bai bufa ba jeki kiyi Aikinki Ai Namiji Banda Tabbas dama ni na fahimce bawani sonki Yake ba, ki kwantar da hankalinki kinji"

"To kaka nagode"

Tana komawa dak'i takira k'awarta Sam tafad'a mata itama hak'uri tabata,.....

  ***********"""""""""""*******

Wash gari duka sun had'e  Abuja A babbar headquarter ta sojojin

Major Sa'id Yafito ya Fara magana bayan Angama zab'ar wad'an da za'ayi tafiyar dasu,

Su 4 ne Abokan juna Samir, Taj, Sam Jidda dama sune suka Jima suna Aiki tare saidai Samir shine babba cikinsu,

"Abunda Yasa namuku kiran gaggawa shine Akwai wata Annoba data fad'a wani gari, kuma ta rutsa da wata Y'ar k'ank'anuwar yarinyar general wadda bazata wuce shekara 3 Shine mukeson kuje ku ceto wannan yarinyar, sanin kunada k'wazo yasa Nasa daku cikin Wannan tafiyar, Wanda Kai Kaine jagoran tafiyar Captain Samir, Amma sanin makamar daji Emanuel ne Dan Haka ko Ina zaku shiga Saida nasa izinin, ga sauran Abokan tafiya ne Duka ku 200 zaku Domin dajin da Hatsari, Akwai makaman YAK'I da muka tanadar muku sosai, sannan duk Wanda Yadawo daga wannan tafiyar to yanada K'arin girma da kyauta ta musamman Wadda kuma shikanshi general zaima mutum babbar kyauta muddin Aka ceto masa Y'arsa kusani tafiyar dolece kuma kada ku kuskura Arasa Y'ar, Magana tak'are zaku iya tafiya yanzu fatan Alheri da nasara"....................

      _BASEERA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

*D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀*

     _PAID BOOK #300 ONLY_

  
     _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

   “`MARUBUCIYAR…  (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d’a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak’in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d’aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA….. And Other’s BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK….(20) SAKACINA PAID BOOK…. (21) SO!!! FREE BOOK… (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR  MIJINA PAID BOOK… (23) D’AUKE D’AI D’AI DUNIYAR SHAID’ANU PAID BOOK
loading….. Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝“`

          _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad’aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had’ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_   *D’AUKE D’AI D’AI DUNIYAR SHAID’ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY*
      _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar….._

*Free 🅿️ 6 to 10*

           …….”Taj nifa jikina yayi sanyi Anya wannan  tafiyar zanyi ta kuwa,”? Cikin sanyi Jidda tayi maganar,

     “Haba Jidda kada ki sare Mana kinmanta irin wuyar da kika shiga Kafin kisami wannan Aikin ma? Kuma Kika samu sannan kikayi training ba iyar wuyar da Baki shaba Amma Kika jure har yanzu Kika kawo wannan matakin bugu da k’ari Bakida kowa sai kaka kaka Bata dogara da kowa ba sai ke ki K’arasa cika burinki Mana Zaki iya,”

  “Amma Taj kaduba irin Yawan makaman da Aka bayar zuwa Sojojinda Aka had’amu dasu wannan kad’an ya isa ya tabbatar inda zamu shiga wurine Mai had’ari,”

“K’awata kada kisaka tsoro kisa su d’auka macce batada jarumta Mana Zaki iya koma meye,”

Hunmm: “Shikenan Allah yabamu nasara”

“Ameen suka Ansa,”

Tinda Suke zancen Samir kallonsu kawai Yake Amma yasan wannan tafiyar saita banbanta da saura kawai shi ba mutum bane ma’aboci yawan magana shiyasa yayi shuru Amma Yana fatan suyi nasara Kan wannan Aikin,….

Suna fitowa waje inda zasu shiga motar saiga bash Yakira Jidda, cikin mamakin ganinsa Nan taje, “Ya lafaya meya kawoka nan? Tafiyar zamuyi fa,”

“Yanzu Jidda saikin je kenan, bazaki fasa ba,”?

“Kaga  mungama wannan maganar tini Anawa tinanin so kabar sauran zancen saina dawo kawai,”

“Idan kikaje bani bake zaj tura A k’arb’o komai nawa, Zan Aure wata daban,”

“Allah ya bada zaman lafiya,” tace cikin Jin haushin maganar tashi tawuce,.

         Taj kuwa tinda taje wurin bash ya kejin wani irin zafi mara misaltuwa take ya b’ata fuska ya fad’a motar yana danna Mata Hon cikin Haushin kula bash datayi,.

     Dariya Sam tayi dama tasani Yana dakon son Jidda kawai ya kasa fad’a Mata ne, domin ganin tana da kayan wani kanta,

Samir kuwa murmushi kawai yayi 

Shiga motar tayi tana Fad’in “Kuyi hak’uri”

Cikin d’aga murya bash Yace”Wallahi I’m serious Jidda idan kikayi tafiyar to munrabu kenan!!!,”

    Wani irin d’aci taji Yana taso Mata tindaga Zuciyarta har cikin bakin ta, wannan ai to zarci ne,

Luummm shi Ido tayi tana Jin zafin maganar shi,

Taj kuwa dad’in maganar tasa yaji Domin koba komai watak’il nasa rabo ne yasa hakan tafaru,

“Idan d’an iskan baijaye daga Hanyar mu takashi kawai,” Cewar Taj cikin d’aga murya,

Satar kallonta yayi still idanta rufe tajingina jikin kujerar motar,.

Tafiya maitsawo sukayi inda suna Amfani da computer zuwa taswirar gano dajin,  basu tsaya ba Saida sukayi tafiya Mai Nisan Gaske kusan sai magriba, Sannan Suka tsaya domin sallah Sunshiga daji Anan suka kafa tinti harda bacci Nan zasuyi sai zuwa safiya sannan suci gaba da tafiyar,.

Masuyin sallah Suka fara, wad’an da basayi kuwa suka Fara cin Abincinsu,

Bayan sungama sallah suka Fara cin Abincinsu

Jidda kuwa zubawa Abincin Ido kawai tayi tana tinane tinanenta,

Cikin sanyi Taj Yace”Jidda Aikinki baya buk’atar dogon tinanin balantana keda Kika shigo babban Assignment, ki daure kici Abincin kinji,”

Hunmm: “nagode da kulawa”

Nan suka kwana lafiya k’alau basu had’u da komai na cutarwa ba,

Ahankali Taj yaie shiga Lamarin Jidda harta rage yawan tinanin,

Kwana 7 sukayi suna tafiyar sun shiga manya manyan da zuzzuka sun wuce birane da garuruwa , Computer tana Nuna musu sun kusa Shiga dajin,

Randa suka cika Kwana 12 suka iso wani dajin Wanda mota Bata shiga inda Taswirar ta Nuna zasubi,

Fitowa sukayi Suna nufar dajin datake Wayoyinsu da Computer suka d’auke komai ya daina Halbawa,

Cikin mamaki Samir Yace”kunga Computer tadaina Aiki hakan Yana Nuna muna cewa Cewa inda zamu shiga ba Network duk wani  Sadarwa baya Aiki wurin,”

“Yaya zamuyi kenan tinda kusan computer itace d’auke da Abun komawar my dama zuwan namu,” Cewar Sam

Taj Yace”Saidai mu d’auke duk wani Abu da zamu iya, Sai kuma muyi Amfani da Taswirar takarda, Yanzu Aikinka zai fara Emanuel”

Cikin Isa da hura Hanci Yafito tsakiyar su Yace, Kowa Yacika wannan cakar da makaman domin kariya wa kansa tinda motar Bata shiga ciki, sannan wannan zagaye nane so dole kumin biyayya,” Yana gama Fad’ar Hakan Yafara lodar nasa makaman A jaka, ganin haka yasa kowa Yafara d’iba,

Tsaki Sam tayi Tace”dube shi kamar wani Birin har yake Fad’in Dole A masa biyayya Mtssswwww”

“Rabuda banza dama ni haushi yake ban wallahi,” Cewar jidda

Murmushi Samir yayi”Kunga ku manta dashi kawai muje mud’iba Muma,”

Kowa ya d’auke Abunda zai iya Koda na lek’a motar Naga sun kwashe makaman dukan ko wanne d’auke da k’atuwar jaka A bayansa Hannuwansu kuwa d’auke da manyan bindigoginsu Suka nausa cikin dajin, Emanuel ne gaba sai Samir, Taj, Sam, jidda sai sauran tawagar tasu ko wanne rik’e da bindiga Kuma A shirye Koda wani Abu zai taso musu,

Sunyi nisa sosai domin sunshiga tsakar dajin ba Abunda Suka gani, bakajin komai sai sautin kukan wasu tsuntsaye Yan tsiraru, ga manya manyan itace dogaye Wad’an da suka ma dajin k’awanya,

Kwatsam sukaji wani irin gurnani na fitowa ta gefensu Yana nufosu,

Cikin tsorata Suka tsaya can bisa d’aga hannu da Emanuel yayi yana wurwurga idanuwa Dan ganin meke Shirin kawo musu far maki,.

Kamar daga sama saiga wani gabjejen Zaki Ya fito, Wanda Sam baida shawar kallo, sau d’aya zaka kalleshi kasan lalle bawai iya zakin gaske wanda Suka sani bane, Dole wannan SHAID’ANIN ALJANINE Yadawo zaki,

Tsaye yayi yana k’ura musu idanuwansa wad’an da jajir suke hak’uransa Zara Zara masu tsinin gaske, Wani irin Gurnani yayi Wanda Saida dajin Ya Ansa gaba d’aya, kansu Ankara Wasu shirga shirgan zakuna kamar sa suka bayyana bayansa,

Tsorata Iya tsorata sun tsorata domin wasu har sun ja baya,

Cikin rawar muryar Sam tace”Bana tinanin bindiga zata iya Kub’utar da rayukan mu dole mu k’ara da takubba,”

Maida bindigar Samir da Sam sukayi zuwa Taj jidda kuwa iya bindigar kawai zata iya rik’awa,

Ganin hakan yasa SHAID’ANUN ZAKUNAN suka fad’a musu da mugun nufi…………………..

Wai koya zata kasance??

Kubiyoni next page Masoyana….

*BASEERATA ITACE ARZIKINA😍*

     WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button