Magungunan musulunci

Magunguna Ta Hanyar Amfani Da Zuma Ga Lafiyar Dan Adam: sabon bincike

ADVERTISEMENT

MAGUNGUNA TA HANYAR AMFANIN DA ZUMA

Bayanin Zuma A Takaice

Kudan Zuma wasu kwari ne ma su daraja, wadanda rayuwarsu take cike da abubuwan mamaki, kuma kudan zuma suna da kaifin basira wajen sani da tsara hanyoyin tattalin arziki, musamman wajen tanadin abincinsu mai amfani gare su

da kuma amfani da waraka ga mutane. Hakika zuma magani ce ga mutane saboda fadin Allah (S.W.T) Q: 16 V:69.

A wani Hadisin Annabi (S.A.W) yana cewa, “Na umarce ku da warkarwa biyu, Alkur’ani da zuma.”

Manyan masanan Musulmai kamar su Ibn Sina da babban masanin nan Malamin tafsiri Fakharur-razi dukkansu sun yi wasiyya da shan Zuma domin waraka ce ga cutuka. Sayyadina Umar (R.A) ya kasance duk lokacin da wani kurji
ya fito masa, to zuma yake shafa masa, kuma cikin ikon Allah albarkacin Annabi sai kaga ya warke. Haka kuma Annabi (S.A.W) ya ce mafi alherin magani zuma, don haka shan zuma yana taimakon kayan cikin mutum su rika aiki a tsare. Shan zuma yana wasashe kwakwalwa ta rika fahimta sosai.

Amfanin Bukurul Sa’adah

Bukurus-sa’adah, shima suna ne na wani turare, shi dai wannan turaren ba abinda yake sawa sai farin jini, matukar mutum ya shafa shi to zai samu farin jini a wajen mutane, kuma za su dinga sonsa, misali in mace ta shafa shi za tayi farin jini sosai da sosai a wajen samari. Ana samunsa a Nagari Bookshop, Kano.

Amfanin Zuma Ga Lafiyarmu A Kur’ani, Hadisi Da Binciken

Kimiyya

Hakika babu wata tantama ga wani Musulmi cewa, Allah ya sanya waraka a cikin zuma. Shekaru dubbai da suka gabata, al’umma ke amfani da zuma a kan cututtuka daban-daban kuma ake samun waraka.

Fiye da shekaru dubu hudu da suka gabata al’ummomi a kasashen duniya ke amfani da zuma don samar da magungunan cututtuka kuma a sami nasara.

Haka al’amarin yake a zamanin fiyayyen halitta Annabi (S.A.W), yayı amfani da zuma, kuma ya yi umarni da ita a kan cututtuka, kuma Allah (S.W.T) ya ba da sauki.

Bayan Kur’ani da Hadisan Ma’aiki sun tabbatar da alfanun zuma ga lafiyar dan Adam. Nazari da bincike mai zurfi game da alfanunta ga lafiya ya gabata, kuma har yanzu ana kan gudanar da wasu, ko da yake a yanzu an samu damar gano da yawa daga irin amfanin zuma ga lafiya kuma har yanzu ana kan gano wasu daga cikin fa’idojinta.

Amfanin Annur

Annur, sunan wani hadadden maganin sanyi kenan da kamfanin As-sa’aadah Islamic Medicine suka hada muku da itatuwa ma su albarka. Yana da kyau ‘yan uwa ku mallaki naku, a shagon Nagari Bookshop ake samunsa.

Mu a wajenmu Musulmai, duk wata fa’ida da binciken zamani ya gano ba wani abun mamaki ba ne a wajenmu, don kuwa tuni Mahaliccinmu da Annabinmu (S.A.W) suka tabbatar

mana da amfaninta ga lafiya, kuma mun yi imanı da hakan, don haka duk abubuwan da za su gano a gare su ne abin yake sabo.

Ba shakka, zuma ta shahara wajen magance matsalolin dan Adam da yawan gaske, kamar su; ciwon ido, ciwon ciki, ciwon mafitsara, tarı da mura da sauransu.

Maganin ciwon ciki da zuma

Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Ya Rasulullahi dan uwana yana fama da ciwon ciki.” sai Annabı (S.A.W) yai mai umarni da yaje ya ba shi zuma, kuma da ya ba shi zumar sai ya warke.

Maganin Olsa da zuma

Mai fama da ulcer ya dinga shan zuma zaı warke da yardar Allah.

Maganin Tari da zuma

Mai fama da tari ya dinga shan zuma, domin binciken zamanı ya tabbatar da cewa shan zuma daidai yake da shan maganin tarı na chemist, kuma itama tana da sinadarin da ke sa barci, sai dai a dinga shan cokali biyu kawai.

Amfanin Dan Asali

Dan’asali sunan wani shahararren magani kenan na fitar da Aljanu daga jikin dan Adam, kuma yana yin kakkarfar kariya don hana Aljanu shiga jikin mutum. Hakika wannan magani yana karya asiri kuma yana yin dafa’i. Don Inganta Garkuwar Jiki Don kuwa garkuwar jiki ita ce ke fatattakar kwayoyin cuta, to shan zuma yana inganta garkuwar jiki.

Kuma zuma tana iya wannan aiki a jiki ne saboda tana kunshe da sinadaran (Vitamin) da (Iron) masu yawan gaske da ke taka muhimmiyar rawa wajen inganta garkuwar jiki.

AMFANIN ZUMA DON KARIN KUZARI

Shekaru masu yawa da suka shude, mutanen da aikin su ya shafi na karfi, ko motsa jiki, kan yi amfanı da zuma don samun karin kuzari da kuma wartsakewa daga gajıya.
Don ko a bincike na wannan lokacin ya nuna hakan, wato tana da sinadaran da ke kara kuzarin jiki da kuma sanya saurın

wartsakewa daga gajiya. Don. samun kuzarin jiki, sai a zuba babban cokali biyu a shayi da safe ko kuma a sha babban cokali na zumar da safe.

MAGANIN KUNAN WUTA DA ZUMA

Shekaru masu yawa da suka gabata, a kasar Misra ana amfani da zuma wajen maganin kunan wuta, ko rauni, idan an samu mai wannan matsala sai a samu zuma mai kyau a dinga shafawa a wajen.

Amfanin ‘Yar Mama

‘Yar marna, suna ne na wani maganin cikowar Hips (mazaunai) mai kyau, kuma original.

Hakika yin amfani da wannan magani zai sa hips din mace su cicciko sosai. Yana da kyau a ce kin mallaki naki.

MAGANIN KAIFIN BASIRA DA ZUMA

Idan ana son samun wannan fa’ida, sai a juri shan zuma kullum, saboda masana sun gano cewa, shan cokali daya na zuma zai samarwa da mutum kaifin basira da kyakkyawan tunani.

Maganin Ciwon Ido ta hanyar amfani da zuma

Ana amfani da zuma wajen magance ciwon ido, ana gaurayata a cikin ruwa mai dumi a wanke idon sau biyu a kullum.

ZUMA NA MAGANIN CANCER

Hakika zuma na kunshe da wasu sinadarai da ke kare jiki daga hadarin kamuwa da cutar (cancer) daji.

MAGANIN CIWON ZUCIYA

Yadda zuma take da sinadaran da ke baiwa jiki rigakafin kamuwa da cutar daji, haka kuma take taimakawa wajen kare jiki daga kamuwa daga cututtukan da suka shafi zuciyar dan Adam.

AMFANIN ADON TAFIYA

Adon tafiya suna ne na wani mashahurin maganin sa nono yai girma (breast enlargement) ‘yar uwa matukar kina bukatar breast dinki yai girma to ki hanzarta mallakar wannan magani, in ba ki samu ba to ki ce a ba ki Umbrella, domin shima umbrella magani ne na sa breast ya mike ya daina kwantawa.

Amfanin ake amfani da zuma don gyara fata

Zuma tana sanya fata tayi kyau, kwarai da gaske, maimakon yin amfani da mayukan da ba a san kansu ba, wasu ma masu illa ne ba mu sani ba, zai fi kyau ayi amfani da zuma don samun kyakkyawar fata.

Yadda za ai kuwa shi ne, a samu babban cokali daya na zuma babban cokali daya na madara a cakuda, a shafa a fuska a kyale shi kamar minti goma sannan a wanke, tabbas yana gyara fata.

Karin Bayani

Kasantuwar kudan zuma yana cin furanni daban-daban, da kuma wasu lokutan yana cin itatuwa daban-daban, hakan ne yasa kashinsa da yake fitarwa ake da yakinin yana magunguna da yawa a cikin jikin dan Adam.

Shi yasa mutane ke amfani da ruwan zumar a matsayin abinci ko magani ga cututtuka da dama.

Haka ma dai an ambaci zuma a wurare da dama a cikin Alkur’ani Mai girma, saboda Allah ya muhimmancinta. nuna mana

Don haka a wajen masana ilimin kimiya a zamanance ma haka abin yake, domin kuwa suma sun tabbatar tana da amfani sosai, mu da ma tuni mun yarda saboda fadin Allah da Manzonsa.

Amfanin Lailatul Urshi

Lailatul Urshi, sunan wani magani ne na karin ni’ima ga mata, hakika mace koda ta kafe ma’ana babu ni’ima a jikinta, to matukar zata yi amfani da wannan maganin zata samu.

Zuma Tana taimakawa mai
Mura,
Tari,
Atishawa da sauran matsalolin sanyi.

Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa.
Tana saukaka narkewar abinci, ga masu fama da rashin
narkewar abinci.
Tana maganin gudawa.
Tana gyara fata da rage kurajen fuska idan ana shafata.
Tana maganin gyambon ciki (ulcer)

Amfanin zuma don karin kuzari

Tana rage nauyin kiba, domin kuwa shan ruwa mai dumi da lemon tsami tare da zuma kafin aci komai da safe zai taimaka wajen rage kiba.

Tana kashe cutar (Vacteria) da (fungas), da kuma ba da kariya daga kamuwa da ciwon daji.

Wasu Daga Cikin Sirrikan Zuma Zuma na kare mutum daga kamuwa da cutar siga (Diabetes)

Zuma na rage yawan mantuwa, musamman matan da suka daina haihuwa.

Zuma na warkar da cutar da take kama hakarkari (Pneumonia).

Zuma na taimakawa mutane maza da mata da ke fama da matsalar rashin haihuwa.

Zuma na maganin ciwon ciki

Zuma na warkar da tari

Zuma na warkar da rauni

Zuma na maganin mura

Zuma na maganin matsalolin ido, kamar jan ido, kaikayin ido, kumburin ido da sauransu.

Amfanin Ramin Kura

Ramın Kura, sunan wani katafaren maganı kenan na karya asırı, in har anyi wa mutum asiri to da zarar anyı amfani da wannan maganı zai karye da izinin Allah.

Wannan maganin yana hana asiri shiga jikin mutum, matukar ana yawan amfani dashi, Amfanın Golden Age

Golden Age, sunan wata zuma ce wadda aka hada ta da itatuwa ma su albarka, wannan zuma tana maganin olsa (gyambon ciki) yin amfani da ita yana maganin ulcer. .

Yana daga cikin sirrin zurna, za ka ji ana yawan cewa a hada wannan maganin da zuma.

Maganın Basirar Yara

Yana daga sirrin zuma in an haifi yaro ya kai kamar wata hudu, kullum a dinga diga masa a baki sau uku a rana, saboda tana kara masa wayo da basira, da kaifin hadda in ya girma sannan tana sa kashinsa ya kara kwari.

DON SAMUN CIKAKKIYAR LAFIYA

Yana daga sirrin zuma, mace mai jego ta dinga shan zuma a kullum itama sau uku a rana, kafin ta haihu da bayan ta haihu saboda samun cikakkiyar lafiya ita da yaronta.

Maganin Ciwon Ciki

Yana daga sirrin zuma, idan mutum yana fama da yawan ciwon ciki mai daurewa, ya dinga karanta Ayatul Kursiyyu kafa
bakwai a cikin zuma yana sha a kullum, in sha Allah zai rabu da shi.

Maganin Kukan Yaro

Yana daga sirrin zuma, idan yaro yana yawan kuka na babu gaira babu dalili, ko yawan kuka idan ya farka daga barci, to a samu zuma mai kyau marar hadi a tofa bismillah Rafa tara a dinga bashi ya lasa, in sha Allah zai daina.

Maganin Tashin Zuciya

Idan mutum zuciyarsa tana tashi, da zarar ya ji zata tashi sai ya dibi zuma cikin cokali daya ya sha, in sha Allah za ta daina tashi.

Don Haihuwa Cikin Sauki Haka nan yana daga cikin sirrin zuma a haihu cikin sauki, in ana nakuda a sha zuma to in sha Allah za a haihu lafiya.

Maganin Warin Baki

Yana daga sirrin zuma, don hana warin baki kullum mutum ya sha da safe bakinsa zai daina wari.

Maganin Fitsarin Kwance Yana daga sirrin zuma, idan yaro yana fitsarin kwance, to kullum a dinga ba shi zuma sau biyu a rana zai daina in sha Allah.

Don Gyara Murya Yana daga cikin sirrin zuma in aka hadata da citta ana sha zai gyara makogwaro, murya ta yi wasai.

CEO for littafan Yaki
Mansur Usman Sufi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button