Magungunan musulunci

Amfanin Zogale Guda 100 ga lafiyar Dan Adam na shekarar 2024

ADVERTISEMENT

 

MAGUNGUNA TA HANYAR AMFANIN DA ZOGALE

 

Bayanin Zogale A Takaice

      Zogale wata ‘yar karamar bishiya ce wadda komai na jikinta tun daga jijiyoyinta, saiwarta, sassakenta, furanninta har ya zuwa ganyenta, kowanne da irin nasa amfanin ga lafiyar jikin dan Adam.

        Idan muka dauki garin ganyen zogale, za mu ga cewa yana dauke da sinadarai kamar haka:-

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Vitamin (A), 

Vitamin (B), 

Vitamin (C), 

Vitamin (E), 

sinadarin zinc, folic acid, inositol, calcium, iron, potassium, selenium, copper, sulphur, da magnesium, 

da dai sauran wasu wanda gangar jikin dan Adam ke matukar bukata.

 

             Zogale daya ne daga cikin nau’o’in abinci masu albarka da Allah ya hore mana, ba domin kawar da yunwa kawai ake cin zogale ba, amfaninta ya zarce hakan saboda dimbin sinadaran da Allah ya zuba a cikinsa masu matukar amfani ga jikin dan Adam.

Sannu a hankali, da yardar Allah zan kawo muku yadda ake sarrafa shi ya zama mai amfani ga jama’a.

 

AMFANIN ‘YAR MAMA

       ‘Yar Mama sunan wani magani ne wanda idan mace tana amfani da shi (Hips) dinta za su yi manya-manya (Hips enlargement).

    Hakika duk wadda take son (Hips) dinta suyi manya-manya to tai hanzarin mallakar wannan maganin, hakika za ta ji dadinsa. Ana samunsa a Nagari Bookshop.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Amfanin zogale na farko 

Fa’ida Ta Daya (1)

         Garin zogale yana taimakawa kwakwalwa wajen bata damar aiki yadda ya kamata. Haka zalika, garin zogale yana kaifafa kwakwalwa da rage yawan mantuwa.

Baya ga haka yana taimakawa jijiyoyin da suke isar da sakon ga kwakwalwa.

Amfanin bushasshan zogale ga lafiyar hanta (2)

      Garin bushasshen zogale na da tasiri sosai wajen bawa hanta (liver) kariya, kuma yana taimaka wa hanta wajen fitar da duk wasu gurbatattun abubuwa da jiki ba ya bukata.

Sannan yana bawa hanta kariya na musamman wajen duk wani abin da zai gurbata ta.

      Baya ga wannan yana hana cutar ‘Fibrosis’ (wani abu da yake fitowa, mafi yawanci a mahaifar mace yayi ta girma har ya hanata samun haihuwa) tasiri a jikin dan Adam.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Amfanin zogale don magance sanyi infection 

       Garin busasshen zogale, na da tasiri wajen magance matsalolin mafitsara, cututtukan sanyi, matsalolin zuciya, tare da taimaka wa gangar jiki wajen warkar da ciwo.

 

Amfanin Umbrella

Wannan magani mai suna umbrella, magani ne wanda yake sa nono (breast) girma, breast enlargement, yana sa breast kyau, sosai kuma ya tsayar da shi.

Yana da kyau ace ‘yanmata da matan aure suna aiki dashi domin zai taimaka musu, za ki same shi a Nagari Bookshop.

Amfanin zogale don magance ciwon sikari 

       Garin busasshen zogale yana taimaka wa masu ciwon sukari tare da hana ciwon tasiri. Amfaninsa bai tsaya a nan ba, don yana rage sinadarin “Cholesterol” da ke cikin jini, tare da ba wa kwayoyin halitta kariya ta musamman.

Samun ruwan nono ta hanyar amfani da zogale

 

    

 

 

 

 

 

 

 

 

  Garin busasshen zogale ga uwa mai shayarwa na da matukar kyau ga lafiyarta, don yana taimaka mata wajen samar da ruwan nono (mama), musamman in’ta jimanci amfani da shi a kullum, hakan zai bai wa uwa damar shayar da jaririnta cikin koshin lafiya ba tare da ta gaza ba.

 

Gyaran fata don amfani da zogale 

       Garin busasshen zogale, yana taimaka wa fatar jikin mutum wajen hana ta bushewa, yamutsewa da karc fata daga fesowar kurajen fuska.

Muddin za ki jimanci amfani da garin busasshen zogale a kullum, to fatarki za ta kasance cikin damshi, haske, sheki, kyau, da kuma kyan gani.

Amfanin Nisa’u Khairan

Nisa’u khairan, shi ne sunan maganin karin ni’ima ga mata, ‘yar uwa ki hanzarta neman sa don ki burge maigidanki.

Yadda ake amfani da zogale har ya yi aiki

Shi ganyen zogale, ba a shanya shi a rana, domin yana dauke da wasu sinadarai wadanda hasken rana ke rage musu karfi da amfaninsu a jikin dan Adam, shi ganyen zogale an fi son a shanya shi a waje mai inuwa, mai tsafta.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Fa’ida Ta Takwas (8)

Hanyoyin amfani da garin zogale na da yawa, amma za ka iya sa garin busasshen zogale a shayi ko koko, ko kunu, ko abinci, ya danganta da yadda ake so ayi tasarrafi da shi.

Maganin Ulcer ta hanyar amfani da zogale (Olsa)

       Ana dafa ganyen zogale a zuba masa zuma asha kamar shayı yin hakan yana maganin olsa (gyambon ciki).

Amfani da zogale don magance 

ciwon Kai

     Ana shafa danyen ganyen zogale a kan goshi domin maganın ciwon kai.

Maganin tsayar da zubar jini da zogale 

       Ga wanda ya yanke ko wani karfe ya ji masa ciwo, to ya

shafa danyen ganyen zogale a wurın, in sha Allah jinin zai tsaya

 

Amfanin Empire

     Empire, shi ne sunan maganin matsı na mata, duk wadda take son ta dawo gam-gam, to tayi amfanı da wannan maganın. Ana samun sa a shagon Nagari Bookshop.

Amfanin A Square

     A Skuare, shi ne sunan wani maganın cutar suga (diabetes) kenan, wanda kamfanin As-sa’aadah Islamic Medicine suka hada muku, don haka duk mai fama da wannan cuta yana da kyau ya mallaka.

Maganin Kuraje ta hanyar amfani da zogale 

        Mai fama da wannan matsala ta kuraje, to kakarsa ta yanke saka, ya hada garin zogale da man zaitun ya dinga shafawa a wurin da kurajen suke.

 

 

 

 

 

Maganin Gyambo

       Mai fama da gyambo, ya sanya garin zogale a kan gyambon, yin haka yana saurin sa shi saurin warkewa.

 

MAGANCE HAWAN JINI DA ZOGALE

    Maganin Hawan Jini Mai fama da hawan jini, in zai ci abinci ya dinga sanya garin zogale a ciki domin kuwa yin hakan yana maganin hawan jini.

 

Maganin Karin Kuzari da zogale 

Mai son karin kuzari, to ya kasance in har zai ci abinci yana sanya garin zogale.

Magance Shawara Da Ganyen Zogale 

       Mai fama da wannan sananniyar cutar mai suna shawara, to Allah ya taimake shi, domin kuwa da magati a tare da zogale, kamar haka:

Ya dafa ganyen zogale tare da sa kanwa ‘yar kadan a ciki domin yin hakan yana maganin shawara

 

Amfanin Champion

Sunan wani maganin cutar cancer kenan mai kyau, duk mai fama da cancer, cutar daji, (sabara) ya hanzarta nemansa.

Maganin Ciwon Kunne Mai fama da wannan ciwon, zai diga ruwan danyen zogale a kunnen da yake ciwon.

 

AMFANIN DA ZOGALE DON SAMUN RUWAN NONO

       Macen da take shayarwa, ta dafa furen zogale da zuma ta rika amfani da shi domin ta samu karin ruwan nono.

Amfanin zogale don magance cutar fitsari 

          Wanda yake fama da wannan matsalar, to ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.

 

 

 

 

 

 

Maganin sanyi da zogale 

         Duk mai fama da sanyi yana da kyau ya samu furen zogale da albasa ya tafasa su ya dinga sha kamar shayi. Hakika wannan hadin yana maganin sanyi.

 

MAGANCE TSUTSAR CIKI DA GANYEN ZOGALE 

          Mai fama da wannan matsalar ya dinga cin danyen zogale, yana maganin tsutsar ciki ga yara.

Maganin ciwon Hanta da zogale 

          Wanda yake ciwon hanta, ya daka ganyen zogale da ‘ya’yan Baure ya sha da nono ko kunu, wannan yana maganin ciwon hanta.

Magance Sanyin Kashi da zogale 

    Wanda yake da wannan larurar, ya samo ‘ya’yan zogale ya soya su, sannan ya dake su, sannan ya hada su da man kwakwar manja ya dinga shafe wajan.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Maganin Kumburi

Mai fama da wani kumburi zai soya ‘ya’yan zogale sai kuma ya daka su sannan a hada da manja a shafa a kan kumburin.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Maganin Tsakuwar Ciki (Apendix)

Wanda duk (apendix) tsakuwar ciki take damunsa, to ya daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana, ya dinga sha da nono. Hakika

 

Magunguna Ta Hanyar Amfanin Da zogale

yana maganin tsakuwar ciki wadda da turanci ake kira da (Apendix).

Maganin Cutar Kanjamau (AIDS) da zogale 

  Mai fama da cutar kanjamau, to ya dinga shan ruwan dafaffen zogale, domin kuwa yana rage radadinsa.

    Magance typoid da maleria da zogale

     Yawan shan ruwan dafaffen zogale yana maganin Typoid da Malaria.

Maganin Basir Da Shawara Hakika shan ruwan dafaffen zogale yana maganin Basir da shawara.

 

KO KA SAN?

  • Zogale na kunshe da (Vitamin C), ninki biyar fiye da lemon zaki?

Yana kunshe da (Vitamin A) har sau biyar fiye da karas Yana kunshe da (Calcium) har sau hudu fiye da madara.

Yana kunshe da (Potasium) ninki uku fiye da Ayaba.

Yana iya maye gurbin kifi da kwai wajen samar da (Proteins).

     Wadannan dalilai yasa ake kiransa da (Miracle Tree) a harshen Nasara, wato bishiya mai abin al’ajabi. Haka nan a kasar (Phillipines) suke kiransa da (Mother’s best friend) wato aminin uwa, ba wani abu yasa ake wa zogale wannan kirari ba, illa saboda matukar aikinsa ga lafiyar dan Adam.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Magunguna Ta Hanyar Amfanin Da Zogale

    Kasar (Phillipines) suna amfani da shi ne wajen kula da yaransu, kuma hakan yakan sa su dau lokaci mai tsawo ba tare da sun kai ‘ya’yansu zuwa asibiti ba.

A kasar India, suna yin amfani da shi ga iyaye mata ma su shayarwa don samar musu da isasshen nono ga ‘ya’yansu.

 

Amfanin Bukurul Ibbi

Bukurul Ibbi, sunan wani turare ne wanda yake matukar sa soyayya, idan mace ta shafa to za aji ana sonta sosai.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ana samunsa a Nagari Bookshop.

Bari mu koma baya kadan, shekaru aru-aru da suka wuce, Likitoci a kasashen Rum, Misra, da Girka, suna yin amfani da zogale wajen magance cututtuka irin su; rudewar ciki, rauni, inganta garkuwar jiki, matsalar zuciya da sauransu.

 

Inganta Garkuwar Jiki

Yawaita cin dafaffen ganyen zogale ko miyarsa yana inganta garkuwar jiki.

Don Samun Lafiyar Zuciya Domin samun lafiyayyen zuciya, to sai a juri cin zogale ko shan shayin da aka hada da ganyen zogale.

Maganin Ciwon Suga (Diabetes) Mai fama da wannan larurar, ya yawaita cin zogale domin kuwa zai matukar taimakonsa sosai.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Maganin Gyaran Gashi Duk wadda take son gashinta yayi kyau, ya kuma daina karyewa to ta rinka amfani da man ‘ya’yan zogale.

Maganin Kara Karfin Gani da zogale 

    Zogale na kara karfin gani, saboda sinadarin (Vitamin A) mai dimbin yawa da yake da shi, haka kuma yana kare jijiyoyin idon daga lahani.

 

Fadakarwa

Jama’a kar mu manta cewa Allah Ubangiji bai saukar da cuta ba, sai da ya fara saukar mana da maganinta.

Hakika zogale magani ne na musamman wanda Allah ya ba mu albarkacin Annabi (S.A.W)..

Allah Yasa mu dace, Amin.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

AMFANIN SAIWAR ZOGALA

Saiwar zogala nada matukar amfani ga lafiyar dan adam domin masana sirrin magunguna sukanyi amfani daita sosae wajen sarrafa magunguna dadama domin riga kafi ko warkar da wasu cuttukan dake addaba alumma amma yanzu zamu kawo maku wasu magunguna da saiwar zogala keyi wanda suka hada da.

 

(1) SANYIN JIKI

A tauna saiwar zogale  tare da citta kwara daya.

 

(2) TSUTSAR CIKI

A tafasa saiwar zogale da jar kanwa a sha.

 

(3) CIWON SANYI 

A tafasa saiwar zogale da kwara daya na tafarnuwa a sha sau biyu ga wuni tsawon kwana uku.

 

(4) YAWAN MANIYYI

 A gauraya cokali daya karami da sachet daya na madara.

 

(5) TARI KO MURA

A gauraya garin saiwar zogale da zuma a sha cokali daya a kullum da safe tsawon sati daya.

 

(6) RAGE NAUYI KO IBA

A tafasa saiwar zogale da lemun tsami daya a tace a sha bayan an karya sau daya a kullum

 

(7)ZAFIN FISTARI

A tafasa saiwar zogale da kanumfari a aha sau uku safe da rana da yamma.

 

 (8 ) CIWON SUGAR

A rinka cin garin saiwar zogale a cikin abinci.

 

(9) QAZUWA

A gauraya cokali daya na garin saiwar zogale da man zaitun a sha 

 

(10) CIWON DAJI CIKIN BAKI

A tafasa saiwar zogale a marmasa gishiri a kurkure baki dashi a kullum sau uku, safe da rana da yamma

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

(11) CIWON YASTA DAN KARKARE

A gauraya kwata na karamin cokali na garin saiwar zogale da na lalle a dorawa yatsan dake ciwo.

 

(12) CIWON KAI MAI ZAFI

A yi hayakin saiwar zogale da garin habba.

 

(13) KARIN NIIMA GA MATA

A tafasa saiwar zogale a tace ruwan misalin kwara daya na karamin cup sai a zuba rabin gwangwanin madara  a sha.

 

Some of The Chemical Composition of Moringa (Wasu daga cikin sinadaran da ake samu a jikin Zogale)

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Magunguna Ta Hanyar Amfanin Da Zogale

Danshi

Danyen furotin

Sodium

Potassium

Selenium

Lenoleic acid

Phosphorus

Palmitic acid

Stearil acid

Bitamin A

Zinc

Folic acid

Selenium

“Copper

Ether ya fitar

Calcium

Ash

Magnesium

Kuercetin

B-caratene

Ascorbic acid

Fatty acid

Bitamin B

Bitamin C

Inistol

Sulfur

Iron

Ma’adinai

Classificar Scientific na Moringa

1) Mulki

– Plantea

2) Sunan dangi

Zogale ce

3) Genus

Zogale

4) Nau’i

  1. Oleifera

5) Sunan Einomial

Moringa oleifera

 

1 Zogale, Bishiyar Ganga, Bishiyar Benzoil

6) Sunan gama gari

Abin da Allah (S.W.T) ya nufe ni da rubutawa ga wannan littafi ya cika, godiya ta tabbata ga Madawwamin Sarki Mai iko akan komai da komai. Tsira da Aminci su kara tabbata ga wanda babu wani Annabi bayansa (S.A.W). Muna rokon Allah Ya yafe mana kura-kuranmu, Ya kuma sanya mu cikin ceton Annabinsa Mai girma, Amin.

CEO for 

Littafanyaki.com.ng

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button