Hausa novels

SIRRIN DAUKAKA Book Compelet Document Hausa Romantic Novels writing by Aisha Jb

ADVERTISEMENT

SIRRIN ƊAUKAKA…!

Hausa Novels Complete

Writing by Aisha Jb


PAGE ONE..


“Baba burina kasha kafini bukata dan Allah.” kawar da kanshi yayi gefe duk da jikinshi baya motsi sakamakon ciwon dake tattare dashi bakinshi ma a karkace yake ƙwalla ne ya gangaro masa da sauri ta ajiye kofin tana share mishi hawaye “Baba na ɓata maka rai ko? toh kayi hakuri insha Allahu bazan kara ba.” a hankali ya soma magana “Jiddah ni baki min komai ba, 

             hasalima bana bukatar komai ya shiga bakina.. da sauri ta dakatar dashi “karkace haka Baba in baka shaba maganin fa? nafi son lafiyanka fiye da komai domin kai da mama kaɗai kuka ragemin kune gata na! kunne bangon da inna jingina ajikinku nake jin daɗi ku kaɗai ne farin cikina kayi hakuri kasha kaga jiya bakaci komai ba.” 

        “Jiddah ina ganin gazawata! ni yadace in fita in nimo muku abinci ni yadace na muku komai keda mahaifiyarki Amma dubi halin da nake ciki kalla fa? jiddah na gaza muku wannan abubuwan gashi dangina wanda ya kamata su tsaya su temakeni duk sun gujeni kowa guduna yake sabida banida kuɗi ni talaka ne!..” kukane ya kwace mishi Mama da fitowarta kenan daga banɗaki ta karaso tare da durkuwa a hankali ta ajiye butan hannunta dakyar ta miƙe sakamakon cikin jikinta dayafara tsufa “Kayi hakuri Allah yana sane damu kuma wannan jarrabawace bawai don baya sonmu bane a’a yayi haƙan ne don ya gwada imaninmu kuma a kullin muna gode masa Allah ya ubangiji Allah kai kayi Adamu kayi hawa’u Allah bamu da kowa bayan kai Ubangiji ka sassauta mana Allah ka kawo mana agaji Alfarman wannan rana ta juma’a kabawa Mijina Usama lafiya” jiddah dake jikin mahaifinta ta amsa da “Ameen mamana. “

Dafa cikinta tayi tare da girgiza kai rabonta da abinci tun jiya shima kanzone wanda jiddah taje makota tayi wanke wanke ta samo musu Allah kenan! me yanda yaso da bawanshi “Asama’u ɗauki kokon nan ki sha.” mama tace. “a ah Usama kai yafi dacewa daka sha domin kasha magani.” usama yace “Asma’u bana son jayayya kin fini bukata bani da burin da yawuce ganin farin cikin iyalina daga shi se bashin Mu’azzan dake kaina inna roƙon ka Allah  ka billomin da hanyar da zan cika wannan burin nawa kafin mutuwata.. “kabarmu dawa usama?. “Akwai Allah..”

                Juyo da kanshi yayi ga Jiddah    “ɗauki ki baiwa mahaifiyar ki Allah ya miki Albarka ubangiji ya tsaremin ke da mutuncinki Allah ya rabaki da sharrin samarin zamani!.” ɗaukan kunnun tayi ta nufo mahaifiyarta dashi “buɗe bakinki nabaki mamana.” ba musu ta buɗe bakinta domi Ɗan cikinta harya fara motsi tsaban yunwan dake cinta cokali kurɓa uku taman kokon ya kare cire kofin jiddah tayi a bakinta Ahankali Asma’u ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata wani irin yunwane ya taso mata.

              Gurgar da kofin Jiddah tayi tana kiran sunanta “Mama mamana meya sameki?.” cizewa tayi tare da faɗin “bakomai Jiddah…” 


                 Shiru suka zauna chan Jidda ta miƙe butan da mahaifiyarta ,ta ajiye ta ɗauka roban fentin da take zuba ruwa ta nufa shuru tayi sakamakon ganin bokitin ba ruwa “Sauran ruwan na zaga dashi.” cewan Mama bokitin ta ɗauka “bari inje in samo ruwan” fatan Alkhairi suka mata bayan ta fita Asma’u ta matso jikin mijinta kwantar da kanta tayi a jikin taburman  da yake kwance “lna son shafa fisƙanki babu halin haka ko zaki temaka ki ɗauki hannuna zuwa ƙan fusƙan taki?” wani irin marayan kuka tasa a hankali sautin kuƙan nata yake fita hannunshi ta kama takai saman fisƙanta amma lna ko motsi bayayi dalilin haka yasa ta kara sautin kuƙan nata “meyasa haka! meyasa wasu mutanen basa duba gobensu! meyasa wasu mutanen suke manta alkhairi ? yanzun sakamakon temakon kenan? usama duk kai kajawo mana wannan masifar meyasa ka Auro mana masifa jubeni da yarintata na koma tsohuwa kalleni… kalli cikina wai yau mune abinda zamuci yake gagarar mu? me muka mata?, takwashe komai Allah kana gani ƴata ba makaranta ko ɗaya Ƴar da zamu ciyar amma i’ta take fita tasmo mana abinda zamuci Yarinyar da bata huci wanka ba amma wai yau i’ta ke ɗawainiya damu Allah ka kawo mana agaji.. “Asma’u kiyi hakuri tausayinta naji gani nayi kowa ya gujeta gani nayi ta fara fusƙantar tsana da tsangwaman mutane kowa ya gujeta bansan haka ze kasance ba na nufeta da Alkhairi amma ta saka min da sharri ta rabani da Ɗana ta ruguzamin komai nawa kalli yanda ta mayar dani, *LAIFINA NE”* (Shima sabon buk ɗina ne yana nan tafe da yardan Allah),


“Asma’u.” ɗagowa tayi taga shima yana hawaye share mishi tayi sannan i’tama ta share na fisƙanta “Jin yanayin da ka kira sunana kaɗai ya shedamun magana kakeso kayi dani me muhimmanci koma menene inna Addu’ar Allah yasa kunnuwana suji Alkhairi..” “Tabbas maganace zamuyi wanda nake so kiyi mata kyakkyawan fahimta ki hangi nesa karki juyawa akalan maganata zuwa baya , ina nufin karki tuna baya domin inhar kikayi haka sheɗan ne ze rinjayeki ki bijiremin wanda inhar haƙan ta kasance bazanci daɗi ba nayi iya tunani da hange hange Asma’u bani da hanyar da zan biya Mu’azzan dubu talatin dalilin haka na yanke shawarar.. “shuru yayi yana nazarin yanayin da zata ɗauki maganan bezata ba, yaji tana faɗin “Kayanke shawarar bashi Auren Hauwa’u koba abinda kakeson cewa ba kenan kayi shuru kanajin tsoron faɗa domin bazan amince bako? shifa mutumin nan baka sanshi ba, babu abinda kuka haɗa matarsa uku kasuwancine ya haɗaku gani nake kuma be damu da kuɗinsa ba domin yanada wanda sukaci uban dubu talatin Hauwa bazata iya ratsa mata uku ta zauna ba wallahi na tabbata zata ci baƙar wahala yarinyar da bata san menene rayuwa ba watan gobe fa Hauwa zata shiga sha-huɗu..” katseta yayi “wake sama da wani cikin neda ke?.” sunkuyar da ƙanta tayi kasa “wakeda ikon zab’arwa Jiddah mijin Aure? cikin nida ke wake da iko da Me-Jiddah? akwai wani bayan ni akwai abinda uba shine adon ƴar sa, mutumcin ƴa mace Gidan mijinta..”


…….”Tabbas Da uba ake Ado, amma kagane man, hauwa bazata iya ɗauƙan nauyin da kake shirin  ɗaura mata ba, kayi hakuri mijina bawai inna jayayya dakai bane a’ah halin da zata tsinci kanta nake tunani Ya zanyi? Na amince…” bata rufe bakinta ba taga mutane suna shigowa “Lafiya? ya zaku shigo mana har ɗaki ba niman izini?..” makalewa sauran maganan yai sakamakon ganin MeGidan dasuke zaune a ciki hannu ya miko mata cikin rawan murya tace “Kayi hakuri Ado.. “Ke Dakata bashi ya kawoni ba kud’i zaku bani banja da tsayi ba, shekara ta zagayo kunce na muku uziri nabarku kun sake wata biyar Kai! Gaskiya ina bukatar kud’i ko abarmin Gidana, domin zan zuba sabbi ‘Yan haya” 


“Ado kasake Kara Mana lokaci wallahi a halin yanzun ko ficika bazaka samu ba abincin da zamuci ma ya gagaremu..” Ado yace abincin da zakaci ma ya gagareka bare dubu takwas ku kwashe komatsansu ku watsar su fita min daga Gida wannan ai zance banzane! ‘yan kayayyakinsu suka shiga kwashewa suna watsar dasu a kofan Gida “Dan Allah kiyi hakuri karku tozartamu ka dubi Allah ka dubi Halin rashin lafiyan da Mijina yake ciki… “Ku jasu ku fitar mun dasu daga Gida bana son Kara ganinsu Kona sak’an d’ayane” (Nayi Alkawari insha Allahu babu turanci a littafina sede in ya zama dole ne, dolenma me  k’arfi).


Tafiya take riƙe da bokiti Gurin d’iban ruwansu na tuka tuka, ta nufa nan ta tarar da Gurin cike da mutane Fam shuru ta tsaya tana tunanin yanda zata tsaya har layi yazo k’anta ga Halin da iyayenta suke ciki matsowa tayi Kusa da Yarinyar da layi yazo k’anta “Ayya ‘yar uwa dan Allah ki temaka ki zuba min nabar Gida IYAYENA duka babu me gamsheshshen lafiyan jiki.” Cikin tausayawa Yarinyar ta karb’i bakitinta ta Tara mata cik’e da murna Jiddah ta Mata godiya sannan ta shiga kok’arin d’agawa har ta d’aura a k’anta “Chabd’i jan ai wallahi Baki isa ba Taya zakiso a Bayan mu sannan kije kid’iba ruwa ai wallahi kinyi kad’an..” yarinyar data zubawa Jiddah ruwa tace “haba Baraka ki dubi Halin da take ciki dan Allah ki rage niman fitina Hauwace fa wanda Da, muke makarantar Allo tare kafin daga baya Allah ya jarrabe mahaifinta da rashi karatunta ya tsaya a halin yanzun ma Yana kwance baya motsi ai ko don Haka kya barta taje Gida.” tsalle baraka tayi “Ke Zubaida ban tambayeki ba, surutu chaaa kaman wani kanari Ina ruwana da jarabta waya jawomusu ba ubanta ba ruwan Nan Kuma wallahi bazaki tafi dashi ba.” Ture bokitin K’an Jiddah tayi take ya fashe ruwan ya zube a kasa Durkusawa Jiddah tayi tare da fashewa da wani i’rin marayan kuka taga samu taga rashi, wannan tozarcin dame yayi Kama? D’agowa tayi ta kalli Baraka ga mutanen gurin Kowa na tur DA abinda tayiwa Jiddah “Ku barta daman haka rayuwa take wannan d’inma yana dagacikin jarrabawan DA Allah ya rubuto mana kije bazan ce Miki komai ba Allahn dayayimu shi kad’ai yasan huk’uncin daze miki ni ban i’sa namiki Abinda Allah be miki ba.” Tana kuka ta karasa maganan tattara bokitin tayi tasoma tafiya Zubaida tace “Hauwa kiyi hakuri dan Allah ga ruwana ki d’auki D’aya.” Carab Baraka tace “Wallahi bazata d’auka ba aje a Haka gayyar tsiya Wanda talauci ya Kare musu…” Juyowa Jiddah tayi tare da fad’in “Me kud’i da talaka duk Allah ne yayisu! Kuma babu Wanda yafi wani a Gurin Ubangiji Bayan Wanda yafi jin tsoronsa da kiyaye dokokinsa Alhamdulillah mu talakawane Kuma bamu dogara da kowa ba se Allahn dayayimu bawai bayason mu bane yayimu a talakawa sedon ya gwada yanda karfin imaninmu yake kefa? Uban naki karkashin mace yake mijin tace! Se abinda uwarki take so yake Mata jikinsa na b’ari ban fad’i hak’an dan ranki ya b’aci ba, in kinji zafin maganata kiyi hakuri Zubaida nagode sosai da tausayawanki gareni.” Tafiyarta tayi Baraka ta kudunduma wata uwar ashar Wanda ni Aysha bazaku jishi abakina ba, domin yafi k’arfi na.

  “Meye abin damuwa da zagi  data Miki ,Bayan ke Kika fara? Ai wallahi Nan gaba duka zakisha Allah ya temakeki Hauwa yarinyace me hakuri wallahi na tabbata da watace Sekin kwashi kashinki a hannu kai lna amfanin fitina?.” Jiddah tana tafiya rumgume da fasassun bikitinta, tana kuka a Haka har ta karaso anguwarsu tun daga nesa ta fara ganin mutane a kofar gidan da sauri ta karaso Mama ta gani Kusa da Mahaifinta tana kuka Bata San lokacin da tayi watsi da bokitin ta karaso gurinsu ba “Baba Mama lafiya meya samu samu baba naganshi a kasa ya kuka fito waje..” kafin mamarta tayi magana Ado yace “Nina sa aka watsar min dasu a waje domin na gaji da ganinku cikin Gidana Dan Haka wallahi ku tattara ku barmin kofar gida Kona Kira muku jami’an tsaro” Wani i’rin kuka Jiddah tasa “Dan girman Allah Baba Ado kayi hakuri wallahi bamuda Gurin Zuwa kan dubi Halin DA muke ciki ka barmu mu zauna Wallahi nayi Alkawari zan biyaka kud’inka.” Tsaf yake kallonta tare da shafa Tunbinsa “I’dan zaki ringa Zuwa D’akina muna kwana tare Har Gidan zan bar muku.” Sunkuyar da kai Jiddah tayi kasa Asma’u tace “Wa’iyazu billahi ‘yar tawa kakeson lalatawa Insha Allahu Allah baze ta’ba baka nasara ba D’an i’ska la’ananne…” Haureta yayi da kafarsa take ta kifu da cikin jikin wani i’rin kara tasa tare da Kiran sunan mijinTa “USAMA.. wayyo cikina mutuwa zanyi” daga Haka Bata karacewa komai ba Da sauri Jiddah ta matso gurinta d’agota tayi tare da d’orata jikinta Kumatunta ta shiga tabawa “Mamana dan Allah ki tashi mama karki tafi ki barmu a wannan duniyan da take cik’e da azzalumai mama Kinga babana banida wasu Bayan ku ki tashi mama karki min haka… “JIDDAH.” DA k’arfi ya Kira sunanta kallon mamarta tayi tare da kallon mahaifinta Ajiye mahaifiyarta tayi tare da rarrafawa gurinshi “Baba kana ganin Abinda sukayiwa mama baba baka iya d’aukan mataki ba? Matarkace fa Wanda nauyinta yake rataye a wiyanka Baba kana kallo sunci mutumcinta sun tafi…”Jiddah Jiddah Jiddah ki kula da k’anki ki tsare mutumcinki duk runtsi karki d’auki d’abi’ar bezo cikin addini ba karkiyi abinda Al’uman musulmi zasuyi tur dake daga karshe Jiddah nayi biyan bashi dake , ki bishi duk inda ya Sanya kafafunsa..” Wani i’rin kunfane ke bin bakinsa Amma duk da Haka be Dena k’okarin mata magana ba, “Allah ya Miki Albarka Allah ya tsare ki..” Baba me kake cewa haka Ya mahaifina! Ka tashi ka motsa gab’ob’inka Muje mu kwaci hakkin mu… A hankali ya sauk’e wani i’rin ajiyan zuciya…

Page2 .

             Tab’ashi take tana kiran Sunanshi Amma shuru baya motsi kwantar da Kanta tayi a jikinshi tana kuka “Yanzun Baba kaima i’rin barcin mama kayi yanzun saura ni d’aya , ku tashi mana kun barni ni kad’ai , nifa bana jin wannan barcin” Limamin anguwarsu ne yazo gurin sakamakon ganin mutane da yayi sun kewayesu “a a lafiya naga kun taru anan meke faruwa?” Ganin Hauwa kwance jikin mahaifinta yasashi faɗin “Hauwa ya kuke zaune a waje?” ɗagowa tayi da sauri tana kuka ta fara labarta mishi abinda yafaru. durkusawa yayi tare da faɗin “Hasbunallahu wani’imal wakeel khai khai! wannan zaluncin har i’na yanzun duk acikin ku babu wanda ze temaka musu kun tsaya ne kawai kuna kallonsu haba! wannan wacce i’rin rayuwace Sekace ba musulmai ba, nasan da ‘Yan uwanku ne Dole nasan se inda karfin ku yakare amma duba Usama ne da matarsa mutum me kirki dason jama’a mutumin da babu ruwanshi da kowa meye amfanin tsayuwarku , Dan Allah ku watse anan!”.

                  d’aya bayan d’aya suka shiga tafiya ya saura mutum uku d’ago Usama yayi yanayinsa kaɗai ya sheda masa rai yayi halinsa Rai bakon DUNIYA girgiza kai yayi yana tunanin rayuwarsu na baya lokacin yana cikin wadata kafin zuwan  wannan bak’ar Kaddaran kai wasu mutanen basuyi ba , rufe mishi idanuwa yayi tare da fad’in “Allah yaji k’anka Usama ubangiji yasa halayyarka nagari subika Allah seya saka muku ka mutu da baƙincikin Ado kuma insha Allahu seyaga karshen sa” Da sauri na ɗago duk da kasancewata yarinya amma ai nasan kalman mutuwa kallon liman nayi ina zare mishi ido “Baban nawa ne ya mutu! Mahifina me sona Babana me K’aunata Babana meson Farin cikina Babana meson ganin dariyata ka duba liman da kyau mahaifina yana raye taya ma ze mutu ya barni ? kullun Babana seyace min Jiddah Allah ya miki Albarka Allah yakare min ke daga sharrin duniya da abinda ke cikinta kullun seya shafa kaina yana faɗin Jiddah burina ki samu ilimi burina kiyi karatun Addini Jidda Ki kasance ‘Ya me biyaya gana sama dake Allah ya bani lafiya nabiya bashin mu’azzan Baralabe anya kuwa babana ze mutu dan Allah liman ka duba wallahi yana barci ne mama kinaji. ki tashi dan Allah baba katashi..!” 

                        wani i’rin kuka mecin rai take tana juya kai seda liman ya zubda kwalla tsaban tausayinta da yamamaye zuciyarsa “Kiyi hakuri Hauwa usama k’an ya rigamu gidan Gaskiya” Kan mahaifiyata na ɗago ina kuka duk na haɗa majina da hawaye na ɗaurata asaman cinyata, hannunta na kama ina matsewa “Shi kenan Liman Babana yace indena Jayayya da nagaba dani, Allah yaji ƙanshi Allah ya kafarta mishi mama ki tashi dan Allah kema karki mutu ki dubeni nayi k’ank’anta da zaman maraici” 


                      Da temakon sauran mutanen dake gurin Liman suka D’auki gawan mahaifina bayan an mishi wanka an suturtashi suka mishi sallah lokacin muna ɗakin matar liman Mama har yanzun bata farka ba sun dubata wai dogon suma tayi har zuwa lokacin da liman yazo yace inje inma mahaifina bankwana amma nadena kuka inhar inna son mahaifina sede na kasa domin ina tuno halin da zamu shiga nan gaba nida mamana haka na daure na mayar da sautin kukan sede hawaye yaki barin fiskata hannu nasa a zanin da aka rufeshi hawaye masu zafine sukaci gaba da biyo k’uncina dakayar na i’ya masa addu’a shima cikin zuciyata domin muddin nace zan fito dashi fili ba shakka kuka zanyi haka innaji inna gani aka ɗauki mahaifina Babana me sona da son farin cikina aka tafi dashi gidanshi na gaskiya shi kenan babu shi an rufe babinsa ya tafi ya barmu bazan sake ganinshi ba ya zanyi da raina ranan haka na wuni kuka sallah ma yinsa kawai nakeyi abinda ya kara ɗagamin hankali har yamma mama bata farka ba, ga zuciyarta na bugawa fisƙanta yayi fayau, gashi mu ba wanda yazo daga dangin mahaifina duk da anje an faɗamusu amma sunki zuwa kirin kirin suka ware mahaifina sabida shi mahaifina shi ɗaya mahaifiyarshi ta haifa ko gurinsu naje se su ringa kyarata basa so na raɓu da ƴaƴansu  dalilin haka nadena zuwa suna sane da halin rashi da muke ciki amma cikinsu babu me temakon mu.. mahaifiyata kuma marainiyace matar liman ta kawo min abinci amma na kasaci domin nariga na saba da zaman yunwa a halin da nake ciki ma wallahi ko nace zanci bazan iya ba,


                       Seda mama tayi kwana biyu kafin Allah ya farkar da i’ta lokacin ina saman sallaya ina sallan la’asar juyawan da zanyi naga tana motsi kafin nace wani abu ta rigani magana abinda ya fito bakinta shine “USAMA cikina ciwo yake min” mezanyi in banda kuka Domin akwai so kauna da Fahimtar juna a tsakaninsu gurinta nazo “Mama kin tashi?” kallona tayi tare da faɗin “Hauwa i’nane nan ina Usama?” kafin na mata bayani  matar liman ta shigo “Masha Allah sannu Asma’u kin farka?” kallonta mama tayi kafin tace “Larai.. Ke Hauwa magana nake dake kina min kuka ina usama yake!” Wani i’rin kuka nasake fashewa dashi duk na kasa mata bayani muryanta ne ya fara rawa alaman i’tama kuƙan take son yi Larai ne ta shiga mana nasiha kafin tace “Asma’u sede kiyi hakuri Usama ya rigamu gidan gaskiya” tun lokacin da Larai ke magana mama tayi shuru tana kallonta cak kuƙanta ya ɗauke wani i’rin abune ya tokare mata makoshi da kyar ta i’ya faɗin “Allahu akbar.. Allah kaji ƙan usama. mijina me kaunata! mijina meson dariya da farin cikina.

                     “Allah ka saukarwa Ado masifa da bala’in dayafi karfinsa Allah ka haɗashi da ajalinsa kaman yadda ya zamo ajalin mijina Allah ka tozartashi kaman yadda ya tozartamu Ya Allah na roƙeka kabani hakuri da jurinyan rashin mijina uban ‘Ya’yana Allah kakai haske da rahama kabarin Usama Allah…” kasa, karasa maganan tayi sakamakon kuka da yakwace mata wanda bata san da zuwansa ba. tana kuka nima inna kuka Larai nata bamu hakuri dakyar na tsayar da nawa kuƙan na kara matsawa jikinta na ɗaura kaina a cinyarta fuskana na kallon nata hawayen idanunta na ɗiga a fiskana.

Hannu nakai fuskanta tare da share mata hawayenta “Ya zamuyi da Ƙaddararmu Haka Allah ya tsara mana Hakuri shine kalman da kullun Baba yake faɗa komai ya fito bakinsa seya haɗa da hakuri se yace muyi hakuri watarana zamuga riban haƙan, sannan duk wanda ya nufemu da sharri mu, mubisa da alkhairi, Mama kiyi hakuri kidena kuka bana son ganin zuban hawayenki hankalina tashi yake..” shuru Asma’u tayi “shi kenan Jiddan Baba nayi shuru Allah ya kara mana juriya da, dangana” 

“Ameen mamana”

                           Kallon larai Asma’u tayi kafin tace “Dan Allah kimin magana da liman” miƙewa Larai tayi kafin tace “Toh” ciƙe da tausayawa Abinci larai ta aiko musu dashi Kallon mama nayi tare da buɗe kwanon samiran tuwon masarane da miyan kuka “Mama kici abinci” girgiza mata kai tayi ” a a Hauwa bana bukatar abinci a yanzun… “Dan Allah mama karkice haka yaushe rabonki da abinci ai ko dan ƙani ko ƙanwata ya kamata kici” lumshe ido mama tayi “Bazaki gane ba, Hauwa ki bar maganan abincin nan kawai..” kuka nasa mata da sauri tace “Ya isa haka zanci” ɗan murmushi nayi kafin nace “yauwa mamana buɗe baki na baki” buɗe bakinta tayi nan na shiga bata tana haɗiya kawai take tana kallona hawaye nabin fisƙanta loma biyar na bata ana shiga ta dakatar dani.

                      “Ya isa haka kema kici” Girgiza mata kai nayi “Base naci ba burina na cigaba da baki har ki koshi..”a a Hauwa kici abinci” rufewa nayi kafin nace “Anjima zanci” Liman da larai suna tsaye suna kallonsu abin sha’awa ya basu ganin yanda yarinya karama take nunawa mahaifiyarta kulawa abinda ya kara birgesu yanda Jiddah ki magana cikin kwantar da murya tare da rarrashi yarinyar da i’ta ya kamata abaiwa wannan kulawar kai! gaskiya Rayuwa ba abakin komai take ba, ta ko’ina Allah yaga dama seya jarrabi bawansa kuma baka isa ka tsallakewa wannan kaddarar ba, Bar ganin Kanada dukiya ka samu duniya kana cinsa yanda kake so kaci me kyau kasha me kyau, ka sanya me kyau kana tafiya cikin isa da izza masu baka kariya nabiye dakai a baya in mota zaka shiga za’a buɗe maka kana zama za’a rufe maka matuƙinka na gefenka duk inda kake so nan za’a kaika mutane na bauta maka sabida dukiya kai kuma a lokacin jin kanƙa kake kafi kowa babu wanda ya kaika zaka taka kowa son ranka! Sufa wanda kake nuna musu isa da izza kake takasu yanda kaso ba finsu kayi ba! domin suma Bani Adam ne kaman yanda kake banbanci shine kai Kanada dukiya, suma in Allah yaso lokaci ɗaya seya kwace naka ya basu nikin ba ninkin naka, Allah yasa mudace Allah ya rabamu da kwaɗayi da ruɗin DUNIYA sallama Liman yayi a hankali Asma’u ta amsa mishi miƙewa nayi naje na kwanko hannuna na dawo “Hauwa in sauran kayan mu na kusa ki duba zaki sami takarda ki ɗauko” hakan kuwa tayi karɓan takardan Mama tayi sannan ta miƙawa malam “Wannan takardan yana ɗauke da sunan Mu’azzan da numbobin wayarsa da adireshinsa mu’azzan nabin usama dubu talatin shekara guda ke nan da watanni babushi babu labarin sa ganin halin matsin da muke cikine yasa usama yanke huƙuncin biyan bashi da Hauwa kafin ya rasu sede ya faɗamin kuma jadda damin nan ta kwashe komai ta faɗa musu sunkuyar dakai kawai nayi inna hawaye “Dan Allah liman ka dubi halin da muke ciki da wanda muke shirin shiga ka samo mutumin nan Hauwa ke kuma kiyi hakuri bamu da yanda zamuyi bamuda shi bamu bawa wani ajiyan sa ba dolence tasa mahaifinki yanke huƙuncin haka” liman yace “insha Allahu zanyi i’ya kokari na gurin ganin na samoshi Allah yaji ƙan usama” da dare ina zaune saman sallaya mama na kwance saman katifan larai duk munyi shuru ga abincin da larai ta kawo mana na dare miƙewa nayi na ninke sallayan tare da cire himar ɗin dana saka “mama abinci” Buɗe idonta da sukayi ja tayi “kici Hauwa inna sane ɗazun bakici ba.. “a a mama ki faraci kafin naci” miƙewa tayi “To shi ƙenan” yanzun ma kaman ɗazun a baki na bata shinkafa da mai da yaji bataci sosai ba ta juyar da kai ruwa na bata ina shirin rufe kwanon ta buɗe nan ta shiga bani dolece tasa nakeci haka ta bani seda ta turamin abincin sosai kafin ta barni. ruwa nasha nazo na kwanta kusa da i’ta Larai na ɗakin liman a haka har barci ya ɗauki mama niƙan idona biyu domin tunda Baba ya rasu na kasa barci tunanin halin da zamu shiga nan gaba nida mahaifiyata da abinde ke cikinta nakeyi domin nasan zaman mu a gidan liman bame ɗorewa bane tun ina kuƙan zuci har ya fito fili ban saniba Hannun mama kawai naji tana share min hawaye na “Ki dena kuka Jiddan baba, Allah yana sane damu be manta damu ba , Hakuri kawai zamuyi mu rumgumi kaddararmu” a daren nan mama tamin nasiha sosai kuka nake wiwi na kasa tsayar da hawayena ashe na bankwana takemin ashe i’tama tafiya zatayi ta barni ta samin albarka tamin addu’a sosai tana shafa kaina tana magana har barci ya ɗaukeni ban sani ba kallona kawai take i’tama barci ya ɗauketa da sanyin asuba ne ya farkar dani har yanzun hannun mama na ɗaure a kaina juyowa nayi na kalli fiskanta tayi fayau se wani haske da tayi zare hannunta nayi nafita naje nayi ɗahara kafin nayi alwala na dawo ɗakin ana kiran sallan asuba naje inna tashin ta “mama lokacin Sallah yayi” a hankali nake magana amma shuru bata amsa min ba ganin haka yasa na taɓata “mama ki tashi haka lokacin sallah yayi” shima shuru kafin na sake magana sega larai “Har kun tashi” a hankali nace “na tashi mama ne take barci ina tashinta taki tashi ma” hannunta larai ta kama nan taji ya sake da sauri ta ɗaura kanta a setin zuciyarta amma ina rai ya riga da yayi halinsa domin kominta baya motsi “innalillahi wainna ilaihi rajiun Allah ya miki rahama Asma’u” bansan lokacin da nayi zaman ƴan bori a kasa ba ɗif nadena jin komai….

Maman Faruq

Book Contact INFORMATION
BOOK SIRRIN DAUKAKA
AUTHOR A’ISHA JB
UPLOADER MRS SUFI NOVELS
IMAGE CREDIT SUFI GRAPHICS
SIZE 1.MB
FILE TXT
DATE 10 JUNE 2024
GROUP ZAUREN SUFI NOVELS
TAGES ROMANTIC  


Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button