RUGUNTUSUMI Book 1 Littafin Yaki Compelet by Abdul’aziz Sani Madakin Gini
RUGUNTSUMI
Book 1 part 1
Rubuta labari
Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
CEO FOR SUFINOVELS.COM
A wani karni na jahiliya a zamanin da mai ƙarfi shi ke da komai an yi wani AZZALUMIN sarki wai shi Jarwal.
Sarki Jarwal yana mulki ne a wata ƙasa da ake ƙira Isnal, a wannan lokaci ba wani gari mai girma da yawan al’umma sama da Isnal, kuma ta zamto cibiyar cinikayyar bayi na arewacin ƙasashen larabawa.
Sarki Jarwal mutum ne marar imani da tausayi domin tun yana ƙarami ɗan shekara goma ya mai da ran bil’adama tamkar na kiyashi. Gashi Allah yayi shi ƙaƙƙarfan gaske. Asalin ƙarfin nasa ne ya janyo ya ci sarautar ƙasar Isnal.
Al’amarin ya faru ne sa’arda ya kashekara talatin da uku, a wannan lokaci Jarwal shahara a wajen ƙarfi da iya yaƙi a duk nahiyar ƙasashen larabawa, domin yana iya faɗa da mutum ɗari ko fiye da hakan a lokaci guda, kuma koda za’a harba masa kibiyoyi guda hamsin ko fiye da hakan a lokaci guda zai iya kaɗe su da takobin hannunsa.
Jarwal yana iya yin gudu da ƙafafunsa cikin jeji har tsawon sa’a shida, ba tare da gaji ba, idan kuwa yana yaƙi ba’a ganin gazawarsa. Domin kusan bayan kowacce sa’a kara samun kuzari yake maimakon gajiya.
Wata rana Jarwal na zaune amahaifiyarsa da yammaci, suna hira sai ya dube ta ya ce “ya Umma daga yau kun daina talauci a garin nan kuma kin daina aikin wahala, sai dai kina daga zaunce ki baiwa bayi umarni su yi miki”
Cikin mamaki tsohuwa Luzaiya ta dube shi tace”Ya kai ɗana ban fahimci batun ka ba, kana nufin zaka kawo bayi ne nan gidan ka ajiye min?”
Jarwal yayi murmushi yace “ba haka nake nufi ba. ina nufin a yau ɗin nan zan zama Sarkin Isnal, zan kashe Sarki Salmanu tare da duk iyalansa na hau karagarsa”
Ko da jin wannan batu sai jikin Luzaiya ya kama karkarwa dan tsananin firgita, ta durkusa gaban Jarwal ta dafa cinyoyinsa tana mai zub da hawaye tace
“Ya kai ɗana ina umartar ka da ka janye wannan manufa domin gaba ɗaya jama’ar Isnal muna ƙaunar sarki Salwan saboda kasancewarsa adalin sarki.
Kowa yana jin daɗin mulkinsa a garin nan, domin baya nuna bambanci tsakanin talaka da attajiri. Ka sani idan ka sauyawa umarnina bani ba kai, kar ka sake tunanin kana da mahaifiya, na sallama ka kenan har abada”
Tana rufe baki Jarwal ya tuntsure da dariya har da faɗowa ƙasa daga kan kujerar da yake zaune, sannanya murtuke fuska ya kama gashin kan Luzayya ta baya yaja da karfi. Ta ji zafi har tayi ƙara, ya dube ta ido da
ido ya ce”Yake ummina kiyi hakuri tun ina ƙanƙani nake da wannan burin, kuma babu wanda ya isa ya hana ni. Tun da haka ne banga amfanin ki ba a yanzu, kin gama aikinki tunda na girma.
Kafin Luzayya ta sake bude baki tace wani abu Jarwal ya murde mata wuya, ta faɗi ƙasa matacciya. Ba tare da ɓata lokaci ba Jarwal yasa ƙafa ya tsallake gawar mahaifiyarsa, ya dau takobinsa ya nufi fada kai tsaye.
Da isarsa gidan sarauta ya hau dakaru da sara hasassautawa, ya dunga ƙoƙarin sai ya kai cikin gidan,ai kuwa dakarun suka yi ta fitowa daga loko-loko na gidan kamar yadda tururruwa ke fita daga raminta sahu-sahu, Jarwal yai ta zubar dasu ƙasa mattattu. Cikin ƙanƙanin lokaci gawa ta yawaita, ko’ina ka duba ita ce fulu-fulu agidan sarautar. Nan da nan labari yaje ga kunnen Sarki Salwanu cewar ga jarumi Jarwal nan ya shigo yana takashe dakaru.
Ko da jin wannan labari sai hankalin sarkiSalmanu ya tashi ya aika wazirinsa ga Jarwal don ya faɗi duk abin da yake so a ba shi.
Yayin da Waziri yazo ga Jarwal sukayi ido biyu sai Jarwal ya dakata da barin kisa, waziri ya dube shi ya ce
“Ya kai Jarumi Jarwal, ka sani Sarki ya aiko ni gare ka, yace ka faɗi duk abin da kake so zai baka amma ka dai na kashe masa dakaru haka”
Yayin da Jarwal yaji wannan saƙo sai ya bushe da dariya sannan yace “Ya kai Waziri ka koma ka gayawa
Sarki cewa bana son komai face ransa da karagarsa, dan haka yayi shirin tunkara ta gani nan tafe gare shi, kuma ‘yan majalisa ku kwantar da hankalinku ba zan kashe ku ba, da ku zanci gaba da mulki a kasar nan”
Ko da Jarwal ya gama wannan jawabi sai ya ɗaga takobinsa yaci gaba da saran masu tsaron gida, yaita kunna kai cikin ƙololuwar gidan har ya isa inda turakar sarki take, aka rasa wanda zai tsaida shi, ko ya kau da shi.
Da ƙarfin tsiya Jarwal ya shiga har cikin turakar ɗakin Sarki, ya iske shi zaune bisa wata shimfiɗa ta mulki, babu ko alamar razana a fuskarsa. Jarwal ya ɗaga takobi yai kansa gadan-gadan zai sare masa kai sai sarki Salwanu yace
“Dakata ba zan roke ka akan kada ka kashe ni ba, amma ina son kayi mini wata alfarma guda ɗaya “cikin mamaki Jarwal yace “Wace irin alfarmace?”
” Ina rokonka da kada ka hana jama’ata yin ibadarsu ta bautar Ubangijin Musulunci a bayan raina, idan kuwa ka ki ina tabbatar maka baza ka dauwama ba akan karaga ba, sannan ka kasance mai adalci gatalakawanka”
Wannan batu yasa Jarwal yayi murmushi yace”Wannan zancen naka dai dai yake da tatsuniyar yara”
Kafin Sarki Salmanu ya kara wani furucin tuni Jarwal ya sare masa kai, kan ya tsinke ya rabu da gangar jiki yai tsalle zuwa can wuri guda, jini ya malala.
Jarwal ya juya ya fita daga ɗakin, take aka kamo dukkanin matan Sarki Salmanu su uku da ‘ya’yayensu goma sha huɗu maza da mata, manya da ƙanana aka kwantar da su aka daddanne masa su ya yi masu yankan rago.
Daga wannan rana Sarki Jarwal yaci gaba da MULKIN ZALUNCI, ma’abota addinin musulunci kuwa a wannan gari na isnal basu ji da daɗi ba, domin sanyawa yayi aka dunga kama su ana gana musu azaba mai radadI, a ce lallai sai sun ce sun fita daga addini. idan kuwa suka ƙi sai a kashe su.
A bisa wannan dalili sukayi hijira a bisa dole suka bar garin. Sai da ta kai ta cewa babu masallaci guda ɗaya a cikin garin Isnal, daga ma’abota bautar gumaka sai masu bautar RANA DA WATA, tamkar ba’a taɓa yin mabiya addinin musulunci ba a ƙasar.
***
Bayan kamar shekara guda da kafuwar wannan masarauta ta kafirci da zalinci, sai wata rana sarki Jarwal yayi wani mummunan mafarki.
A cikin mafarkin aka nuna masa wata ƙanƙanuwar itaciya tayi tsiro, ma’ana ta hudo ƙasa ta baiyana, a hankali itaciyar tarinka girma har ta riƙa sosai, itaciyar asalinta daga
cikin gidan sarautarsa ta fito, amma sai aka wayi gari babu ita, bayan wani ɗan dogon lokaci kuma sai ta sake zuwan ta baiyana a cikin gidan Sarki Jarwal ta dunga fille kan dakarunsa, sai da ta ƙarar da su duka, ta kama shi ta ɗaɗɗaure shi da saiwoyinta. Saboda zafin ɗauruwar da yayi a jikinta take ya suma, koda ya farfaɗo sai ya ganshi a tsakiyar filin fada, duk jama’ar garin sun taru ana kallonsa.
Bishiyar tai magana tace “Ya ku jama’ar Isnal shin kuna son wannan azzalumin sarkin naku, ko bakwa sonsa?”
Gaba ɗaya jama’a suka amsa da cewa “Ba mason sa domin mun gaji da zaluncinsa.”
Bishiya tace “To ga shi ga ku duk hukuncin da kuka ga dama kuyi masa”
Ko da jin haka sai jama’a suka debi duwatsuka suka yi ta jifansa, cikin ƙanƙanin lokaci su kai fata-fatada jikinsa, jini yai ta zuba.
Koda Sarki Jarwal ya zo nan a cikin mafarkinsa, ya ƙwalla ihu mai firgitarwa.
A wannan lokaci yana kwance ne tare da wata matarsa mai suna Kursu. Cikin firgita Kursu ta farka ta ƙanƙame shi tana mai tambayarsa me ya faru. Sauran dakarun gidan kuwa suka rugo da gudu har izuwa wannan daƙi.
Cikin sauri sarki Jarwal ya miƙe yasa tufafinsa, ya dubi dakarunsa da matarsa Kursu yai shiru bai ce komai ba.
Dukkaninsu suka sunkui da kawunansu ƙasa.
Kursu tace “Ya sarkin sarakan duniya, me ya faru gare ka? Na rantse da girman mulkinka na tsorata sosai, saura ƙiris mu yi asarar cikin nan dake tare dani”
Jarwal ya dube ta yai murmushi, sannan ya dubi dakaru ya ce “Aje a kirawo min Boka Zarbalu”.
Cikin gaggawa suka fice suka bar shi tare mai ɗakinshi a tsaye.
“Wani mummunan mafarki na yi wanda tunda na zo duniya ban taɓa yin irinsa ba, haƙiƙa mafirkin ya tsorata ni domin na shiga zulumi da tunanin wai shin mene ne manufarsa?”
Ko da Kursu taji haka sai tayi ajiyar zuciya gami da ƙyakƙyatawa da dariya tace “Haba SARKIN SARAKAI kar kayi abin kunya mana, yanzu ashe mafarki kayi, ai a zatona wani abin tsoro ka gani muraran.
Ashe har akwai wani abu da zai iya firgita ka a cikin faɗin duniyar nan. Ka tuna fa a halin yanzu babu wani Sarki mai ƙarfin mulki kamarka a duk faɗin ƙasashen larabawa dake
duniya”
Ko da jin wannan ziga sai Jarwal ya bushe da dariya yace “Na rantse da tsafi zancen ki gaskiya ne”;
Rufe bakinsa ke da wuya sai ga Boka Zarbalu ya bayyana
Zarbalu ya zube ƙasa yai gaisuwa ya ce “Gani gare ka ya SARKIN DUNIYA, lafiya ka tura a kirawo ni a cikin tsakar dare haka?”
“Ina fa lafiya? Ai ka san ban taɓa turawa a kirawo ka ba a cikin irin wannan lokaci, don haka ruwa ba ya tsami banza,
Nan take Jarwal ya kwashe labarin mafarkin da ya yi ya sanar da Boka Zarbalu.
Yayin da Zarbalu yaji wannan al’amari sai yai shiru bai ce komai ba har izuwa wani ɗan gajeran lokaci, sannan yai ajiyar zuciya ya ɗago kai ya dubi Sarki Jarwal yace
“Ya Sarkin Sarakan duniya, idan ba za ka damu ba zansa ka bini mu tafi izuwa kogon tsafina, domin nayi cikakken bincike na sanar da kai ainihin fassarar wannan mafarki naka.’
Batare da wata gardama ba Sarki Jarwal ya amince da wannan shawara. Nan take suka fita daga harabar gidan, aka kawo keken doki suka hau, aka kai su can bayan gari inda kogon tsafin Boka Zarbalu yake. Kogo ne na baƙin dutse mai tsananin zurfi da tsayi, wanda bashi da ƙofar shiga, ma’ana ko’ina a rufe yake da duwatsu kamar ba a taɓa shiga cikinsa ba. In banda boka Zarbalu babu wani mahaluki da ya taɓa shiga cikin wannan kogo, face wani aljaninsa wanda ake yiwa laƙabi da Zamzanu. Aljani Zamazanu shahararren baƙin kafirin aljani ne wanda ya shahara a duniya a wannan zamani, ba don komai ya shahara ba sai don tsananin girman halittarsa da kuma ƙarfin damtsensa, sai da ya zamana duk aljanun duniya sunashakkarsa maza da mata, musulmai da kafirai.
Shi dai Zamazanu usulinsa ya fito daga jinsin musulmi, amma daga baya sai ya kafirta sabodala burin da ya fi so ya ci zali, ko yai kisa.
A bisa wannan ɗabi’ar tasa ne iyayensa suka yi tsine masa albarka sa’adda yai furucin ridda da bakinsa. wannan lokaci Zamazanu ya shiga duniya ya ciga da zaluntar aljanu da bil’adama a doron ƙasa har ya gamu da boka Zarbalu wanda shi kuma saboda tsantsar hatsabibancinsa da ƙarfin shirin na tsafi ya sa dole Zamazanu ya zama bawansa.
In banda boka Zarbalu babu wanda ya isa ya sa Zamazanu aiki yayi a doron ƙasa. A halin yanzu Zamazanu ne ya ke gadin wannan kogon tsafi na boka Zarbalu.
A bakin kogon wata fadama ce wacce dole sai an bi ta cikinta sannan za’a isa cikin dutsen kogon. Ya yin da sarki Jarwal da boka Zarbalu suka iso bakin wannan fadama, sai suka sauka daga kan doki, sarki Jarwal ya dubi Zarbalu yace
“Wai shin ina ne inda kogon tsafin naka ya ke?Na ga sam babu alamar wani kogo a duk faɗin filin nan.”Ko da jin wannan tambaya sai boka Zarbaluya tuntsure da dariya yace “Ya sarkin duniya ai wannan dutsen da kake gani a gabanmu shi ne kogon tsafina”
Cikin matuƙar mamaki Jarwal ya sake duban Zarbalu yace “To ina kofar shiga? Kuma ta ina za mubi mu ƙetare wannan fadamar?”
Zarbalu yai murmushi yace “Kai dai zuba ido ka sha kallo, hala ka manta kana tare da sarkin matsafan duniya ne?”
Kafin Jarwal ya sake faɗin wani abu sai bokaZarbalu ya rintse idanunsa biyu ya hafa tafin hannayensa biyu waje guda ya daga su sama yace “Buɗe mana ƙofa ya Zamzamanu, samar da hanya garemu ya Zamzamanu, yau muna da babban baƙo”
Ko da fadin hakan sai gaba ɗaya wannan ruwan fadamar ya tsotse a cikin ƙasa kamar yadda mutum ke zuƙe ruwa kofi guda, shi kuwa wannan kogon dutsen sai ya tsage a tsakiya, a hankali ƙofa ta dunga buɗewa da kaɗan-kaɗan har ta kai faɗin da dawaki ɗari za su iya wucewa ta ciki a jere lokaci guda. Da yake tsakaninin inda su Jarwal ke tsaye da ƙofar kogon bai fi kamu biyar ba suna iya hango abubuwan dake cikin kogon daga farko.
Nan take kwakwalwar Sarki Jarwal ta kwance.
tunaninsa na saurin barin duniya ya yanke, sakamakon tarin tsabar dukiyar da ya hango a cikin wannan kogo.
Ba komai ya gani ba face tarin akwatunan ƙarfe marassa adadi cike da lu’u lu’u, jauhari, zinari da zubarjadi. Saboda tsabar cika kowacce akwati taƙi rufuwa, an barta a buɗe, domin dukiyar tayi amai har ƙasa, ko’ina ka duba ita ce baja-baja.
Koka Zarbalu ya dubi Jarwal yace “To zo amma da kai kaɗai za mu shiga, waɗannan bayin masu rakiya su jira mu a waje.
Zarbalu ya waigo ya dubi bayin Sarkin ya ce “Kada ɗayanku ya kuskura ya biyo mu, in kunne yaji gangar jiki ta tsira”Yana gama faɗin haka ya juya yai gaba, sarki Jarwal ya bi shi a baya kamar jela, zuciyarsa cike da ɗumbin tunani da shawarwari.
RUGUNTSUMI
Book 2 part 1
Rubuta labari
Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
CEO FOR SUFINOVELS.COM
Abu na farko da ya fara zuwa zuciyar Jarwal itace wai shin me wannan tsohon Bokan ya ke nema a duniya, alhalin yana da wannan tarin dukiya wacce yai imanin duk duniya ba za’a sami mai rabin ta ba? Wai shin me zai hana ya kwace dukiyar ta zama tasa?T a yaya zaka kwace dukiyar ba tare da ka kashe shi ba? Tabbas ka san takamarka ba ta wuce ta ƙarfi ba, in kuwa haka ne Boka Zarbalu ba zai kasu a hannunka ba, to idan ma ka sami damar kashe shi ɗin, wannan mafarkin da ka yi fa? Wane ne zai iya fassara maka shi? Idan ma an fassara maka ɗin wane ne zai iya tsare ka daga sharrin dake cikin mafarkin? Boka Zarbalu ne kaɗai zai iya warware maka wadannan matsaloli, don haka ya zama wajibi ka bi shi, ka lallaɓa shi har ka sami
damar aiwatar da bukatunka nan gaba.
Wannan shine irin abubuwan da Sarki Jarwal yayi ta sakawa cikin zuciyarsa.
Bayan Sarki Jarwal da Boka Zarbalu sun isa cikin kogon tsafi har sun ƙule, sai ƙofar ta rufe kai kace tunda aka halicci dutsen a haka yake bai taɓa motsi ba. Shi kuma ruwan nan na fadama wanda ƙasa ta tsotse sai ya sake ɓulɓulowa daga cikin ƙarƙashin ƙasa yaci gaba da gudu kai kace idon teku ne.
A wannan lokaci ne bayin nan da suka rako su Jarwal su biyu suka dubi juna, ɗayansu ya dubi ɗan’uwansa ya ce
“Ya kai Zarkal ka sani cewa yau mun samu shekaru kusan ashirin kenan muna bauta a gidan sarauta har yau bamu mallaki ko da doki guda ba. Gashi yau da idanunmu munga dukiyar da ba mu taɓa gani ba, a cikin kogon can. Me zai hana baza muyiwa kanmu gata ba? Mu je mu kwashi iya abin da zamu iya ɗiba mu kama gabanmu, in yaso sai mu gudu mu bar ƙasar nan, ka san dai duk inda mu kaje a duniya dole a girmama mu, don mu zama attajiran da babu kamarsu. Kaga shike nan sai mu auri zukazukan mata. ko da ‘ya’yan sarakuna ne kuwa, mu zauna mu ci duniyarmu da tsinke. Yayin da Janjamu ya zo nan abayanninsa sai Zarkal yai ajiyar zuciya yace
“Lallai Janjamu sai yau na tabbatar da cewa kai wawa ne, ko da ya ke ban sani ba ko duniya ta ishe ka haka shi yasa kake neman ka kai kanka ga mahallaka, shin ɗazu da me ka rufe kunnuwanka har ka kasa jin kashedin da Boka Zarbalu yai mana? Cewa fa yayi
Kar mu kuskura mu bi su izuwa cikin kogon.
To idan mun ƙi bin umarnin ta yaya za mu shiga ciki kogon, alhalin gashi kana gani ƙofar ta rufe, fadamar kuma ta sake tare hanyar?”
Wannan mai sauƙi ne in dai ka amince da shawarat
a, ni na tabbatar da mun faɗi abin da BokaZarbalu ya faɗa ɗazu ƙofar zata sake buɗewa da kanta kuma wannan fadamar zata ɓace”
Mu haɗu a littafi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen littafi.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe
Abdul’aziz Sani Madakin Gini