Karni Uku book 1 by Mansur Usman Sufi
KARNI UKU Book 1
Writing by
MANSUR USMAN SUFI
SARKIN MARUBUTAN YAƘI
08137237071
ƘASAR MADINATUL-BARNAWIY
Kasaitaccen ɗakin taron ya cika ya batse da manyan sarakuna,Bokaye,matsafa haɗe da jarumai.
Duba ɗaya zaka yi musu ka fahimci cewa akwai wani muhimmin al’amari daya taru a wajen.
Tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali babu wanda yace ƙala.
Daga bisani ne wani dattijo ma’abocin ƙasumba da gemu farare sol!, Mai ɗauke da yanayin ɗaure fuska.
Yayi gyaran murya ya dubi jama’ar dake ɗakin taron yace “yaku yan uwana sarakuna da sauran mahalarta wannan taro mai albarka, dafarko ina yiwa kowa Barka da zuwa.
Babban abinda ya tara mu anan shine tabbatar da tsafi a doran ƙasa, wanda hakan bazai taɓa tabbata ba face an ɓatar da ma’abota addinin Musulunci a doran ƙasa.
Sanin kanku ne cewa dakushe hasken musulmi abune mai matukar wahalar gaske, matukar muna son cimma wannan buri namu dole sai mun jefa musulunci cikin saɓon Ubangijinsu.
Daga lokacin da na fara wannan nazari da sauran Yan uwana sarakuna, mun fara cimma nasarori masu yawa, sai dai a halin yanzu ne zamu kama aikin gadan-gadan ta hanyar haɗa karfi da ƙarfe, domin masu iya magana na cewa hannu ɗaya baya ɗaukar jinka.
Ubangiji na faɗa a cikin littafinshi mai tsarki cewa “idan Musulmi suka bauta mashi yadda yake so, zai basu rayuwa mai daɗi tare da ‘ya’yansu da jikokinsu.
Sannan a sunnah ya tabbata cewa su musulmi kamar ginin daƙi ne mai kusurwa huɗu, kowace katanga tana karfafawa ne da yar uwar ta, ma’ana dazarar rabuwar kai ta shiga tsakaninsu kodai ta fahimtar addini ko kabilanci da al’adun yau da kullum,to daga nan zasu samu nasara murƙushe.
Lokacin da dattijon da ake kira da suna urwat ɗan Abbas yazo Nan azancenshi sai dukkan wanda ke cikin ɗakin taron ya cika matukar mamaki jin yana karanta littafin Allah tamkar yakasance musulmi.
Urwat ya cigaba dacewa “Dukkaninmu yan uwa ɗaya ne kuma dangi ɗaya, koda akwai babban jinsi da birane,amma kada mu manta abune ɗaya ne ya haifemu shine, tsafi, bautar gumaka.
Fiye da shekaru arba’ina lokacin ina samartaka, ina rayuwa.
A cikin musulunci,babu wani abu nasu dabani da sani a kanshi walau ta fuskar ilimin addini ko zamantakewa.
Lokacin da yazo nan a jawabinshi sai dukkan wanda ke cikin ɗakin taron ya cika da matuƙar farin ciki,urwat ya gyara zama bisa kujerarshi ya, shiru ne ya kuma mamaye ɗakin taron a karo na biyu.
Sarki sha’aran yayi gyaran murya yace “Bayan dukkan bayanin da sarki urwat ya kawo yanzu, akwai waɗansu muhimman abubuwa da ya kamata mu lura dasu anan, mafi yawan suna burin ganin sabon al’amari na cigaba a wajen su koda ta hanyar karama(almara).
Ko kuwa ta ƙirƙira, bazasu taɓa damuwa ba koda ya saɓa da addinin su zasu ƙarɓeshi hannu biyu, har wasu ma na ganin idan malami baya karama,to bai cika mai tsoron Allah ba.
Yanzu dukkan shiryen mu sunyi nisa, mun tura dukkannin mutanenmu izuwa biranen manyan dauloli musulmi, bayan sun samu horo akan dukkan da muka ɗora su akai, daga cikin nasarorin da muka samu.
Akwai kwaɗaitawa mata da son wassanni, koyarwa da mata dubarun zama da mazajen su na tsarin zamani da al’adunmu, Domin gurɓata zaman su da mazajensu,
Sannan duka Littattafan da muka wallafa Dake yaƙar gaskiyar dake cikin addininsu, yanzu abinda ya rage mana a gaba shine a mako mai zuwa zamu tura rukuni na ƙarshe daga jama’armu ta zasu tafi ƙasashen a matsayin yan gudun hijira, waɗanda a cikin su ne zamu basu muhimman makamai masu barazana ga dukkan wata halitta mai numfashi, gami da sirrikan tsafi.
Lokacin da sarki sha’aran yazo nan azancenshi sai yayi kowa dake ɗakin taron ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa.
Daga wannan kowa ya tattare tawagarsa ya fice daga ɗakin taron.
*****
Yanayin gidan sarautar ya ƙawatu ainun da fiye da misaltawa, idan mutum yakai dubanshi izuwa ga wani ɓangare da yafi ko ina ƙawatuwa zai yi arba da kuyangi,barorin,hadimai gami da dakarun shirye cikin shigar yaƙi na ta kai komo,suna aiyuka.
Wata kuyanga ce matashiya ɗauke da kayan marmari dangin ridda, ayaba da jini, a cikin wani kwandon kaba, ta doshi wata turakar, tana iso masu gadi suka bude mata kofar shiga ta kunna kai izuwa cikin gami da yin sallama.
Shiru taji batare da an amsa mata ba, kuma tana iya jiyo alamun motsi a turakar,haka dai ta cigaba da tafiya sannu a hankali tana huce kofofin turkar, har ta iso inda take sa rai zataga gimbiya.
Salati gami da tasbihi ta dunga karantawa a ranta, har idanun ta sun fara cikowa da kwalla, tana mai runtse su tamkar tayi arba da mutuwarta ƙirjinta na bugawa da sauri,ta saki kwandon dake hannun ta kayan marmarin dake ciki suka tarwatse ta hanyar watsuwa a turkar.
Duk da motsin da ya bayyana na tarwatsewar kayan marmarin, bata sanyasu dawowa cikin hayyacinsu daga saɓon Ubangijinsu ba.
Da sauri ta juya domin komawa da baya, zuciyar ta cike da matuƙar ɗimauta, taya ya za’a aikata wannan mummunan saɓon Allah a gidan sarautar musulunci, tabbas sai na bayyana wannan al’amari ga mai martaba sarki koda kuwa hakan zai zamo ƙarshen numfashina a duniya.
Haka dai ta cigaba da tafiya da sauri har tana tuntuɓe, domin ta isa hanyar da zata sadata da fada.
Fadar ta cika ta batse da manyan fadawa, talakawan gari haɗe dakaru, kowa na zaune cikin ladabi da girmamawa.
Sarki Anwar na zaune a bisa karagarshi ta mulki,sanye da tufafin alfarma irin na hamshaƙen sarakai, hannunshi riƙe da cazbaha,yana jan addu’o’i,
Ana tafiyar da sha’anin mulki cikin lumana.
Wani dattijo ma’abocin tarin shekaru da cikar kamala yayi gyaran murya cikin ladabi ya dubi mai martaba sarki yace”ya shugabana ina wani labari da na samu daga shugaban masu kula da hidimar masallaci cewa, kwana biyu an samu raguwar matasan mu wajen fitowa sallar asubahi, Haƙiƙa hakan babban abin takaici ne sosai,a shawarata kodai a faɗakar da iyaye illar Hakan ko kuwa a sanyawa dukkan wanda yaƙi fitowa sallar asubahi haraji matsawar bada wani uzuri da addini ya amince dashi ba.
Wani mutum daga cikin fadawan sarki da shekarunshi basu gaza arba’in ba, yayi gyaran murya yakawo Gwauron numfashi ya ajiye ya dubi dattijo mai suna Salman yace” Allah ya shugaban majalissa a rawa fahimtar a cikin littafi da sunna, babu wani waje da ake iya tilasta mutum ibada, ballantana ace idan yaƙi yi a sanya mashi haraji, domin ita ibada ana yin ta ne cikin daɗin rai .
Ko da jin wannan batu daga bakin Hakimi urwat sau fadar tayi shiru tamkar mutuwa ta kawo ziyara, duk wannan tattaunawa da ake yi sarki yana ji bai ce uffan ba, sai da ya fahimci tattaunawar zata haifar da damuwa, sai yayi gyaran murya yace” yaku fadawana kuyi sani cewa wannan magana da shugaban majalisa ya kawo na da matukar muhimmanci ainun sai dai ni akwai wata matsala dake ganin tana gaba da wannan kuma dare da rana da ita nake tashi,wannna matsala ba wata ba face yawaitar yan gudun hijira daga waɗansu birane dake zuwa wannan ƙasa tamu, domin samun mafaka, hakan baya rasa nasaba da tashe-tashen hankula da ake samu a birnin Nuraniyyu.
A makon da ya gabata labari ya riskeni cewa a wannan makon an kai wani mummunan hari a masallaci a lokacin da ake gudanar da sallar asubahi, tabbas wannan abun baƙin ciki ne da damuwa daya kamata mu kula sosai ta hanyar ƙarfafa tsaro tare da ba wa mayakan mu horon yaƙi.
Uwa uba kuma shine tsayawa bisa tafarkin da magabata suka ɗora mu akai…..!
Kafin sarki ya ƙarshe maganar sai ya hango kuyanga ihsan ta shigo fadar hankalin ta a tashe tana haki,tamkar numfashinta zai ƙare.
Sarki Anwar ya mayar da dubanshi izuwa gareta domin yaji shin mene ne ke tafe da ita.
Lokacin da yazamana cewa saura taku huɗu tsakanin ta da karagar mulki sai ta zube ƙasa bisa gwiwoyinta ta kwashi gaisuwa.
Sarki ya ƙarɓi gaisuwar cikin annuri.
Ihsan ta buɗi baki ta buɗi baki da nufin tace wani abu amma koda ta haɗa idanu da Hakimi urwat sai taji bakinta yakasa furta komai, tsawon daƙiƙa ashirin tana ƙoƙarin hakan amma ya gagara, Al’amarin da ya sanya sarki da sauran jama’a suka cika da mamaki kenan bisa ganin tana magana da Yaren kurame.
Sarki ya dubeta yace” yake ihsan shin ina dalilin wannan hali da kike ciki, me kike son fahimtar dani?.
Hawaye ne ya shiga shata ta daga idanun ta bisa ganin halin da take ciki, tana mai tambayar kanta akan ranta tana mai mai cewa shin ina dalilin rashin yin maganata, koda wani ne yayi mini wani sihiri, amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenan.
Urwat ya saci kallonta gami da murmushin mugunta, wanda waziri ne kaɗai ya lura da hakan.
“Ta yiwu akwai wata rashin lafiya ce ta same ta, ranka ya daɗe ina ganin yana da kyau mu tafi zuwa masallaci domin lokacin sallar azuhur yayi.
Hakimi urwat ya faɗa cikin ladabi”.
” Zancen ka dutse yakai urwat”.
Sarki ya faɗa tare da kallon in da hasken rana ya ratso a fadar.
Ya ɗorawa batun shi da cewa “A kai ihsan izuwa wajen ‘yar mai ganye domin a duba lafiyarta, Ka dawo da ita izuwa gareni, haƙiƙa na tabbata akwai wani muhimmin al’amari da take son sanar dani, domin na aminta da ita matuƙa.
Ya ƙare zancenshi yana duban wani bafade, saurayin mai yanayin kazar-kazar dake tsaye a hannunshi na dama.
” An gama ya shugabana Bafaden ya daɗi cikin ladabi, ya juya ya nufi kofar fita daga fadar taɓa mai yafito ihsan da hannu dake yi mata nuni ta biyo bayanshi, Da sauri ta miƙe tsaye tayi koyi dashi suka kule izuwa wajen fadar.
Sarki ya sauko bisa karaga ya taka matattakalar fadar ya sauko ƙasa ya durfafi wata kofa ta musamman dogare da sandarshi, dakaru,hadimai tare da hakimai suka mara mashi baya, sauran jama’a sukayi koyi dasu, domin isa zuwa masallaci.
Kafin a isa masallaci sai Hakimi shaibat ya shafi wani gurin tsafi a damtsen hannunshi na dama ya ɓace ɓat!.
Sarki shaibat ya juya domin ya amsa sallamar da wani mutum yayi mashi, ai kuwa sai idanuwanshi suka sauka a saitin inda Hakimi shaibat ke tsaye a can gefenshi, take yaga wayam Babu alamun shi, Batare da bari wani daga cikin jama’arshi ya lura
Bai bayyana ako ina ba sai a daf da kofar fita daga gari, kai tsaye ya durfafi kofar, yayin da dakaru suka hangoshi sai suka miƙa gaisuwa gareshi tare da yi masa sallama yana amsawa, waɗansu dakaru a gefe ya hango sun tare waɗansu samari uku da fuskokin suke ke rufe da bakin rawani suna ɗauke da waɗansu bujjuna a bisa kan amalanke.
Sannu a hankali yana takawa har ya isa gare su.
Mene ne ke faruwa ana ?
Urwat ya tambaya a taƙaice.
Wani saurayi mai tarin ƙasumba ya risina gareshi cikin ladabi ya buɗi baki Muryar na rawa yace ” ya shugabana muna binciken buhhunan da suke ɗauke da sune domin tabbatar da tsaro.
“Shin baka da sanin cewa dukkan kayan daga gareni suka fi to?”.
Urwat ya tambaya fuska a murtuke.
Tuba nake ranka ya daɗe insha Allah hakan bazai sake faruwa ba.
Badakaren ya faɗi.
Cikin hanzari samarin suka tura kayan suka huce gaba.
Badakaren ya bisu da kallo yana ƙarewa buhhunan kallo yana son fahimtar wani abu, har suka ɓace gareshi ya daina hangoshi.
Wata unguwa urwat ya nufa data saɓa da wacce samarin uku suka bi, da shigar unguwar ya durfafi wani gida yana isa tamkar an san da zuwanshi aka wangame kofar gidan ya kunna kai ciki.
Zaune ya isar dasu suna shan barasa suna ta ƙyaƙyata dariyar mugunta, samarin uku da ya baro a hanyar kofar gari ne
Waje ya samu ya zauna bisa wata kujera yana mai fuskantar su a lokacin da suka nutsu domin suji bayanin dazai yi musu.
Ina fatan dukkan kayan mu mun kammala yadda ake buƙata?
Urwat ya tambaya.
Wani daga cikin matasan mai yanayin shiru- shiru shine ya yiwa sauran samarin biyu Indiya ta wutsiyar idanu, da sauri suka miƙe tsaye suka nufi bangare a ɗakin sauko waɗannan buhhunan suka zo suka ajiye a daf da inda urwat yake suka buɗe buhhun.
Urwat ya ɗora idanuwashi akan buhunan domin yaga abinda ke ƙunshi a ciki.
Motsin alamun sawaye suka ji na kusanto da ɗakin, al’marin daya sanya dukkanin su sukayi turus kenan domin ganin abinda ya bayyana gare su zukatansu cike da matuƙar al’ajabi domin kuwa a iya sanin su babu wanda ya san da wannan gida na sirri face su huɗun kacal.
Wannan shi ne abinda ya wakana a ƙasar madinatul-barnawiy.
****
Al’amarin Bafade da ya tafi da kuyanga ihsan izuwa gidan ‘yar mai ganye domin zartar da umarnin mai martaba na duba lafiyarta.
Lokacin da suka kaɗaita a cikin turkar ‘yar mai ganye sai Bafaden ya zayyane mata dukkanin saƙon da yake ɗauke dashi izuwa gare ta daga wajen mai martaba.
Ko da jin wannan batu sai yar mai ganye ta ƙura wa ihsan idanu kuma ta hanya hannunta ta gwale idanun ta na dama, bayan ta kammala bincikenta, sai ta dubi Bafaden ta buɗi baki cikin murya mai tattare da alamun dattijantaka tace.
“Dukkanin ƙoƙarin da nayi domin na gano irin nau’in cutar dake damun ihsan hakan ya fasƙara, Kawai abinda na ɗan fahimta shine an yi amfani da sihiri ne a lalurarta.
“Ni kaina ina zargin hakan matuƙa.
Bafaden ya faɗi.
“Yanzu Ina ganin zan gwada yi mata addu’o’i ku Allah zai sa a dace.
‘yar mai ganye ta faɗa, gami da sanya hannunta ta buɗe bakin ihsan, ta shiga karanta Ayatul-kursiyyu tana Tofa mata a ciki.
Lokacin da ta kammala karatun bisa mamaki sai suka ji ihsan tayi Atishawa da ƙarfi ta buɗi baki tace “Alhamdulillah.
Nan fa Bafaden da ihsan suka cika da matukar farin ciki maral misaltuwa suka yi salati ga Annabi s’a’w domin nuna godiya ga Allah (SWT).
Su kayi sallama da yar mai ganye domin komawa ga mai martaba sarki.
Mu hadu a Karni Uku littafi na biyu kuma na karshe
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
08137237071